Home / Big News / Katukan Tsafe Sun Hadu Da Obasanjo A Landan

Katukan Tsafe Sun Hadu Da Obasanjo A Landan

Daga Imrana Abdullahi
A ranar Litinin 20 ga watan Yuli na shekarar 2026, Injiniya Dokta Abdullahi A Tsafe ( katukan Tsafe), shugaban ma’aikatan Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar ( Marafan Sakkwato), Sanata mai wakiltar Mazabar Zamfara ta Yamma,ya samu alfarmar haduwa da tsohon shugaban kasa a Tarayyar Najeriya,Cif Olusegun Aremu Okikiola Obasanjo, inda suka hadu a filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan da safiyar Litinin din.
Wannan haduwar ta sanya shugabannin guda biyu da ake matukar girmamawa da suka dade suna bautawa Najeriya tare da shugabantar jama’a.
A wannan hoton za a iya ganin Obasanjo daga hannun Dama tare da Katukan Tsafe a hannun Hagu cikin ƙananan kaya.
Muna yi wa Injiniya Dokta Abdullahi A. Tsafe fatan samun ci gaba a dukkan harkokin rayuwarsa da samun gagarumin ci gaba tare da neman kiyayewar Ubangiji madaukakin sarki ya sa aje lafiya a dawo lafiya.

About andiya

Check Also

INDEPENDENCE: UBA SANI FREES 27 INMATES, CLEMENCY BENEFICIARIES EXCEED 500

  Governor Uba Sani of Kaduna State has granted clemency to 27 inmates in correctional …

Leave a Reply

Your email address will not be published.