Home / Big News / Gwamna Uba Sani Ya Dauki Jerry Adams A Matsayin Mataimakin sa

Gwamna Uba Sani Ya Dauki Jerry Adams A Matsayin Mataimakin sa

Daga Imran a Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Kwamared Sanata Uba Sani ya bayyana sunan Jerry Adams a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben shekarar 2027 mai zuwa.
 A yau ranar 28 ga watan Yuli na shekarar 2027 Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya sanar da sunan Jerry Adams da ya fito daga yankin Kudancin Kaduna a matsayin wanda zai yi masa mataimakin Gwamnan.
Gwamnan ya ce ya dauki wannan matakin ne domin ci gaba da samun zaman lafiya da yan uwantaka a tsakanin al’ummar jihar baki daya ta yadda kowa zai tabbatar ana damawa da shi.
Bayan mun yi tuntuba tsakanin al’umma tare da tattaunawa mun yanke hukuncin cewa mun dauki Mista Jerry Adams,FCTI,FNIM,CBA a matsayin wanda za mu yi takarar shekara 2027 da shi a matsayin mataimakin Gwamnan.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.