Daga Imrana Abdullahi
Mista Jonathan Danbaki shugaban kungiyar shugabannin makarantun Sakandare ta Kasa reshen Jihar Kaduna ( ANCOPSS) ya yabawa Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani bisa irin yadda yake kokarin yin gyara da inganta harkokin makarantun Sakandare a Jihar.
Jonathan Danbaki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan kammala taron ya’yan kungiyar karo na 68 da aka yi a dakin taro na dandalin tunawa da marigayi Murtala da ke cikin birnin Kaduna.
Jonathan Danbaki ya ce hakika a wannan zamani na da Gwamna Uba Sani ke jagoranci a Jihar Kaduna makarantu na ganin ayyukan ci gaban jama’a ta hanyar ilimi.
” Muna ganin irin ayyukan da ake yi a makarantun jihar Kaduna na ci gaban ilimi da al’ummar kasa baki daya, saboda haka muna yin kira ga jama’a da su sake zaben Gwamna Uba Sani a karo na biyu ta yadda za a samu damar ci gaba da ayyukan raya ƙasa da ilimi a dukkan fadin jihar baki daya”.
Danbaki ya kuma yi kira ga iyayen yara da su guji daukar ya’yan su zuwa wadansu kasashen waje domin karatun da za su yi, domin babu wata kasa a nan nahiyar Afirka da ya kai Najeriya saboda a koda yaushe duk wadanda suka yi karatu a Najeriya sun fi yin zarra da fice a ko ina suka samu kansu.
Mista Danbaki ya bayyana taron kungiyar na bana karo na 68 da aka yi a Kaduna a matsayin wani al’amari gagarumi da ke cike da dimbin ilimin zamani musamman ta fannin yanar Gizo domin kara inganta harkar ilimi ta yadda duk wanda ya halarci taron zai amfanar da dalibai da sauran jama’ar da yake zaune a cikin su.
THESHIELD Garkuwa