Daga Wakilin mu
Hukumar Hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa ta samu wata gagarumar nasarar kama wata tsohuwa mai shekaru 101 da Hodar Koken da aka kukkula a cikin wani makunshi da ake kira Fufu, inda suka ce sun samu nasara ne bayan gudanar da bincike a wurare daban daban.
Kamar yadda hukumar ta ce sun samu nasarar ne bayan samun ingantattun bayanai na sirri abin da ya ba su damar gudanar da aiki a dukkan hanyoyin tashar ruwa a satin da ya gabata.
Kamar yadda hukumar ta NDLEA ta bayyana tsohuwar yar shekaru sama da dari mai suna Esther Ogunmabo,da aka kama a ranar 15 ga watan Ogusta, a Ilisan, cikin jihar Ogun da kanabis mai nauyin kilogiram 90 da ake kira Skunk,da aka yi wa kananan kulli.
Daraktan bangaren yada labarai tare da fadakarwa na hukumar Femi Babafemi,ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.
Babafemi ya ce tsohuwa Ogunmabo, ta shaidawa masu bincike cewa ta fara harkar miyagun kwayoyi ne bayan da shagon ta ya kama da wuta ta kara da cewa yarta da ta zauna a Legas ake zargin cewa ita ke kawo mata miyagun kwayoyin.
Shugaban Hukumar ta NDLEA Birgediya Janar mai ritaya Mohammed Marwa ya bayar da umarnin cewa a saki tsohuwar a matsayin Beli a kuma rika yi mata aikin fadakarwa tare da wayar da kai duk saboda irin yawan shekarunta, amma an kama yarta domin gudanar da bincike.
A wani aikin kamen kuma da aka yi a Jihar Akwa Ibom, jami’an hukumar a ranar 21 ga watan Ogusta,sun kama wani kwale kwale irin na Katako da ake zargin ana amfani da shi ne wajen safarar miyagun kwayoyi zuwa ga wadansu mutane masu sana’ar kamun kifi a Kamaru.
An kuma kama wadansu da ake zargi su Uku da suka hada da dan shekaru 27 mai suna Kingsley Effiong John,da aka kama da Hodar Koken mai nauyin kilogiram 20 da aka boye a cikin kunshin Gudu.jami’an sun kuma gano kilogiram dari 435 na Kanabis, yayin da yawan jimlar nakotin da aka kama suka kai nauyin kilogiram 42.622.
Yayin da hukumar ta ce ta kama kayan maye na Loud da kudin ya kai naira biliyan 4.4 daga kwantenoni biyu a tashoshin ruwa na APaPa da Lekki a Legas.
Hukumar ta NDLEA ta bayyana samun nasarar kwace miyagun kwayoyin na farko da aka kwace miyagun kwayoyin da aka shigo da su Najeriya ta tashar jirgin ruwa daga Thailand.
A tashar jirgin ruwa ta APaPa, sun samu nasarar kama kayan maye na Loud mai nauyin kilogiram 1,090.5 da aka boye a cikin kulle kullen saces dubu 2,181 a cikin kwantena da aka yi karyar cewa wai Busasshen Kifi ne, Shinkafa,kayan safaya fata,Sabulu da batirin inbata.
An kuma kama wadansu miyagun kwayoyin mai nauyin kilogiram dari hudu 400 da aka samu a wata kwantena a Kalli da aka boye a karkashin rim na takardu 798 mai fadin A4.
Hukumar sun kuma bayar da rahoton cewa sun kama kwayoyin tiramadol da aka boye a cikin kunshin sako (waybill) a cikin mota kirar Bus daga Enugu zuwa Zuba.tuni dai ana kama mai kayan a garin Kontagora jihar Neja.
A jihar India, jami’an hukumar sun lalata miyagun kwayoyi na Hodar kanabis mai nauyin kilogiram dubu Goma (10,000) da aka samu a wata Gona mai hekta hudu a dakin Ijare, an kuma samu wasu metafetamin da kanabis da aka samu a cikin wata motar da aka tsare da ke da nauyin kilogiram 1.325 a wata motar da aka tsare a kan titin Ogbomosho a tagwayen titin Ibada a Jihar Kwara.
Hakazalika kuma hukumar ta kama wata mata mai shekaru 65 a Ibadan jihar Oyo, da kayan maye mai nauyin kilogiram 4.68 da suka hada da loud, Tiramadol, Koden, Diyazafam da Fulunitizefam.
Hukumar kuma ta gudanar da wani kame a Kano,da yankin Seme a jihar Legas da Abiya abin da ya taimaka masu suka kama miyagun kwayoyi da dama da suka hada da Loud, Hodar Kolorado da Tramadol tare da Refnol.
Bayan kamawa tare da kwace miyagun Ababen kayan mayen da aka kama hukumar NDLEA ta ce suna kuma yin aikin fadakarwa a karkashin shirin yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi,da ake yi a makarantu, wuraren addini da kuma shugabanni a jihohi daban daban.
Shugaban hukumar na kasa Buba Marwa ya yaba wa ma’aikatan nasa da suka gudanar da binciken a wurare daban daban, sai ya shawarce su da su kara himma wajen gudanar da aikin su ta yadda za a samu magance matsalar safara da ta’ammali da miyagun kwayoyi a lungu da sako na kasa baki daya.
THESHIELD Garkuwa