Daga Imrana Abdullahi
An bayyana cewa kungiyar Alhaji Atiku Global Concept Mobilization 2027 ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin ba Atiku Abubakar Kuri’u Miliyan Talatin a zaben shugaban kasa mai zuwa .
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi wanda shi ne shugaban kungiyar na kasa ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga jama’a a wani kwarya kwaryan taron da aka yi a Kaduna.
“Kungiyar ta shirya bayar da Kuri’u Miliyan biyar daga Jihar Kano,Kaduna miliyan uku, Zamfara miliyan daya da rabi, da dai sauran Kuri’u masu yawa duk a lokacin zaben 2027 mai zuwa idan Allah ya kai mu.
” Duk mun rigaya mun rarike ko’ina da ko’ina musamman tun daga can kasa zuwa ko’ina duk mun fadakarwa da jama’a komai don haka sai Atiku Abubakar.
“A halin yanzu muna ta kokarin tabbatar da samu da fadakar da jama’a wadanda ke da Kuri’u na gaskiya da za su bayar da Kuri’un a lokacin zabe da za su kai tun daga misalin Jihar Kaduna zuwa Jihar Adamawa, wanda hakan ba karamin al’amari na ne”.
THESHIELD Garkuwa