Home / Labarai / Sarkin Kano, Hajiya Fatima Sun Ƙarfafa ‘Yan Kano Su Mallaki Hannun Jarin Dangote Refinery Domin Gina Makomar Tsararraki

Sarkin Kano, Hajiya Fatima Sun Ƙarfafa ‘Yan Kano Su Mallaki Hannun Jarin Dangote Refinery Domin Gina Makomar Tsararraki

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa  Muhammadu Sanusi II (PhD) da Daraktar Yanki kuma Babbar Mashawarcin Aliko Dangote, Hajiya Fatima Wali Abdurrahman, sun yi kira ga al’ummar Kano da su yi amfani da damar sayen hannun jarin Dangote Refinery wajen gina dukiya da samar da makoma mai inganci ga kansu da ‘ya’yansu.
Yayin da Mai Martaba Sarkin Kano ya mai da hankali kan buƙatar ‘yan Kano su shiga cikin kasuwar hannun jari (Capital Market), Hajiya Fatima ta jaddada muhimmancin iyaye su fara tunanin makomar ‘ya’yansu ta hanyar zuba musu hannun jarin da zai iya bunƙasa rayuwarsu nan gaba.
Sarkin ya bayyana cewa mutanen Kano sun daɗe suna a harkokin kasuwanci da samar da arziki, amma ba su cika  shiga kasuwar hannun jari ba kamar yadda suke shiga sauran harkokin kasuwanci.
Saboda haka, ya ƙarfafa su da su yi amfani da wannan dama ta Dangote Refinery, yana mai cewa kamfanin da Aliko Dangote ya kafa yana da alaƙa ta musamman da Kano, domin shi ɗan Kano ne.
Ya ce: “Dangote Refinery tamu ce. Aliko Dangote namu ne. Kuma Shi ɗan Kano ne.”
Mai Martaba ya bayyana cewa shiga hannun jarin ba wai kawai batun sayen wani abu ba ne, illa wata dama ce ta mallakar wani ɓangare na babban kamfani da kuma koyon wata sabuwar hanyar gina dukiya.
A nata ɓangaren, Hajiya Fatima Wali Abdurrahman ta mayar da hankali kan makomar ‘ya’ya, inda ta shawarci iyaye da su yi la’akari da sayen hannun jari domin ‘ya’yansu, su bar jarin ya bunƙasa tare da lokaci.
Ta ce irin wannan tanadi zai iya taimakawa wajen biyan bukatun ‘ya’ya a nan gaba, musamman wajen ilimintar da su da gina rayuwarsu.
Hajiya Fatima ta kawo misalin yadda Aliko Dangote ya gina makomar ‘ya’yansa ta hanyar ba su ingantaccen ilimi, tarbiyya, da horo a harkokin kasuwanci, inda a yau suke rike da mukaman daraktoci a sassa daban-daban na kamfanoninsa.
Ta ce iyaye ba sai sun sayar da gidaje, gonaki ko wasu kadarorinsu ba kafin su fara zuba jari.
Maimakon haka, ta bukaci su fara da abin da suke da shi, gwargwadon ƙarfinsu, domin su samu damar gina abin da zai iya zama wani ɓangare na makomar ‘ya’yansu.
“Ba sai kun sayar da kadarorinku ba. Ku fara da abin da kuke da shi, gwargwadon ƙarfinku. Ku yi wannan zuba jarin domin makomar ‘ya’yanku, kuma da yardar Allah ba za ku yi nadama ba,” in ji ta.
A yayin da Sarkin Kano ya ƙarfafa al’umma su faɗaɗa sanin kasuwancinsu zuwa kasuwar hannun jari, Hajiya Fatima ta nuna yadda irin wannan zuba jari zai iya zama wani ɓangare da iyaye zasu tanadar wa ‘ya’yansu makoma.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka Yayin Da Zamfara Ke Cika Shekaru 30

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.