Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Tumbuleke Dan Hajiya Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tumbuleke Dan Hajiya Rasuwa

 

Daga Imrana Abdullahi
Bayanan Da muke samu daga cikin garin Kaduna na cewa Allah ya yi ma Alhaji sani Gwarzo, da aka fi sani da Tumbuleke Dan Hajiya Rasuwa yau din nan za’a yi jana’izarsa a Gidansa da ke Layin Adamawa cikin Garin Kaduna a yau ranar sha daya ga watan Ogusta, 2026.
Bayanan da muka samu daga wani makusancinsa ya ce ya rasu ya bar mata daya kuma ya na da shekaru Tamanin da Uku a duniya.
Kuma ya rasu ne a asibitin Gwamnatin jihar Kaduna da ake kira Nursing home cikin garin Kaduna da misalin karfe hudu na Yamma kuma an yi jana’izarsa da misalin ƙarfe biyar da rabi na Yamma a Kaduna.
Marigayi Tumbuleke dai sanannen mutum ne a farfajiyar wasan kwaikwayon Hausa tun tali- tali
Allah ya yi mashi Gafara ya kuma albarkaci abin da ya bari amin

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka Yayin Da Zamfara Ke Cika Shekaru 30

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.