Daga Imrana Abdullahi
Akalla Malaman Islamiyyu da na Allo dari biyar 500 ne Suka amfana da Baburan Hawa Daga Kakakin Majalisar Tarayya Dokta Abbas Tajuddeen.
Shugaban Majalisar Dokokin Tarayya Abuja Dokta Abbs Tajudeen Iyan Zazzau, Ya ce wannan rabon tagomashin Yana Daga Cikin bangaren Ci gaba da tallafawa al’umar karamar Hukumar Zariya don Ganin sun Samu saukin rayuwa da kuma anfana da romon mulkin dimokaradiyya,
Idan za a iya tunawa Malaman Makarantun boko na Firamare dana Sakandare Fiye dubu Biyu ne Suka Samu Baburan Hawa daga shugaban majalisar wakilai.
Haka zalika Dai-dai kun Mutane da kungiyoyi Suna na Daga Cikin wanda Suka anfana a wanchan Karo yayinda ayanzu kuma Malaman Addini suma Yakamata su sheda.
Wanda Suka anfana sunfito Daga bagarorin Izala da Darika don Yiwa Kowa Adalci Cikin wakilcin Iyan Zazzau Tajudeen Abbas.
A jawaban Wakilan Malaman Makarantun Allo dana Islamiyyu Sun Nuna Jindadinsu da Godiya ga Iyan Zazzau bisa samun wannan tagomashi Haka zalika sun jaddada Goyon bayansu gareshi.
Akarshe Tajudeen Yayi Jan Hankali da kada Wanda ya sayar da nashi Sai Kuma sauranda Basu samuba su kara Hakuri suma Insha Allah Nasu na tafe indai sunada Rabo.
A karshe ya roki jama,a da su kara baiwa Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da Gwamna Uba Sani da Sauran yayan Jam,iyyar APC Goyon Baya don ci gada da mulkin da ke Kawo Ci gaba Baki Daya, musamman a Zaben da ke tafe na Shekaran 2027.
THESHIELD Garkuwa