Home / Siyasa / Tafiyar Atiku Abubakar Nijeriya Na Neman Mafita Ne – Suleiman Shinkafi, shugaban kungiyar Alhaji Atiku Global Concept and Mobilization

Tafiyar Atiku Abubakar Nijeriya Na Neman Mafita Ne – Suleiman Shinkafi, shugaban kungiyar Alhaji Atiku Global Concept and Mobilization

…..Atiku Ne Mafita A Najeriya, inji kungiyar AAGCM
Daga Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Alhaji Atiku Abubakar Global Concept and Mobilization na kasa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi Sarkin Shanun Shinkafi na farko ya bayyana kungiyar a matsayin wadda za ta gudanar da yakin neman zabe da ba a ta ba yin irin sa ba a Najeriya.
Suleiman Shinkafi ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da kungiyar ta yi domin ƙaddamar da sababbin shugabanni na kasa da kuma na Jihar Kaduna da aka yi a babban dakin taro na Gombe JOWEL a cikin garin Kaduna.
Dokta Shinkafi ya ce za a yi shiri ne na musamman da za a rika bin kwararo kwararo sako – sako lungu lungu mutane dauke da bututun magana mai kai magana Nesa, (Laud Speaker) ana fadakar da jama’a muhimmancin zaben Atiku Abubakar domin ya zama shugaban kasa a Tarayyar Najeriya.
“Za mu samar da dalilai a ƙalla guda 50 da suke bayanin muhimmancin zaben Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa kuma za mu samar da dalilai guda 50 duk a rubuce da suke bayanin kada a zabi Bola Tunubu duk za a gabatarwa da yan Najeriya irin wadannan dalilai cikin ikon Allah”, inji Dokta Shinkafi.
Ya kara da cewa mun kuma yi shirin zagaye kasar nan jiha bayan jiha duk domin tallata manufofin Atiku Abubakar kowa ce jiha muka je za mu bayar da bututun magana da jama’a za su shiga kwararo kwararo sako Da lungu suna fadakar da jama’a muhimmancin a zabi Atiku Abubakar shugaban Najeriya domin shi ne masanin makamar aikin.
An kuma mikawa shugaban kungiyar Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi takardar kama aiki a rubuce a matsayin shugaba tare da wadansu daga cikin shugabannin duk an ba su takardar kama aikin su a wurin taron na Kaduna a gaban dimbin jama’ar da suka taru a wajen taron.
An kuma bayyana Alhaji Atiku Abubakar a matsayin hayaki fudda na Kogo domin kamar yadda kuka sani honarabul Sa’idu Gombe Dan takarar majalisar Jiha daga Kawo Dan PDP ne amma kuma a sama ya na tare da wannan tafiya sai Atiku.
Tsohon kadan Najeriya kenan a kasar Misra ke mikawa Suleiman Shu’aibu Shinkafi takardar kama aiki a matsayin shugaban kungiyar Alhaji Atiku Global Concept and Mobilization a wajen taron kaddamar da sababbin shugabanni na kasa da reshen jihar Kaduna
Sai kuma Ni Suleiman Shu’aibu Shinkafi Ni dan jam’iyyar APC ne na rike matsayi sosai tun daga Jiha har sama amma duk mun ce sai  Atiku kawai domin kawai kowa na neman mafita ne kuma shi ne masanin hanya.
Wadansu jama’a da dama sun gabatar da jawabai a wajen taron da suka hada da sakataren kungiyar da kuma gabatar da wasan kwaikwayo daga kungiyar masu wasan kwaikwayo a Jihar Kaduna.

About andiya

Check Also

Ana Yi Jam’iyyar APC Saboda Kabir Masari – Ai’sha Mashi

Daga Wakilin mu a arewacin Najeriya Wata yar Gwagwarmayar Siyasa daga jihar Katsina a Arewacin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.