Home / MUKALA / Ibrahim Masari Ya Fi Kowa Tasiri A Wurin Tunubu – Bincike

Ibrahim Masari Ya Fi Kowa Tasiri A Wurin Tunubu – Bincike

 

Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya zama ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da suka fi tasiri a Najeriya.

Tun daga lokacin da ya kasance a bayan fage na harkokin siyasa, musamman bayan rawar da ya taka a matsayin “mai riƙe gurbin mataimakin shugaban ƙasa” (placeholder) ga Tinubu kafin zaɓen 2023, inda aka sanya sunansa a matsayin abokin takarar wucin gadi, Masari ya fara samun ƙarin tasiri.
A yau, ya zama ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da ke tafiyar da harkokin siyasar da suka shafi Shugaba Tinubu, musamman wajen shirye-shiryen siyasar shugaban ƙasa.
Binciken da wakilan jaridar suka gudanar ya nuna cewa Masari na daga cikin ‘yan siyasar da suka fi kusanci da Shugaba Tinubu a Arewacin Najeriya.
Sai dai majiyoyi sun shaida wa Weekend Trust cewa kafin wannan lokaci, irin wannan tasirin siyasa yana hannun Sanata Abu Ibrahim, wanda Tinubu ya fara saninsa tun lokacin da dukansu suka kasance Sanatoci a shekarar 1992, kuma tun daga lokacin suka ci gaba da kasancewa tare da kusanci.
Akwai kuma wasu da suka taɓa zama gwamnoni tare da Tinubu tsakanin 1999 zuwa 2007, ciki har da George Akume, Joshua Dariye da Ali Modu Sheriff, waɗanda suke da matakai daban-daban na kusanci da shi.
Amma bisa ga bayanan majiyoyi daban-daban, Masari ya zama sabon babban ɗan siyasar da Tinubu ke dogaro da shi a Arewa.
Daga “placeholder” zuwa mai ba Shugaban Ƙasa shawara
Bayan tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, an miƙa sunan Ibrahim Kabir Masari ga INEC a matsayin abokin takararsa na wucin gadi.
Daga baya aka sauya wannan tsarin, inda Kashim Shettima ya zama mataimakin Tinubu na dindindin.
Masari ya ja gefe, yana cewa hakan zai bai wa Tinubu damar samar da sarari wajen haɗa buƙatu da muradun ƙungiyoyi da mutane daban-daban.
Wannan matakin ya sa aka fara samun ƙarin haske da magana a kansa a matakin ƙasa.
Bayan Tinubu ya lashe zaɓen 2023, an naɗa Masari a matsayin Senior Special Assistant on Political Affairs, sannan bayan shekaru uku aka ɗaga matsayinsa zuwa Special Adviser on Political Affairs.
Ƙaruwar tasiri da kuma ce-ce-ku-ce
Tasirin Masari ya ƙara bayyana ne lokacin da Shugaba Tinubu ya kira shi da “My Waziri” a gaban wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewa.
Kalmar Waziri a al’adar Hausawa tana nufin wani babban matsayi mai kama da Firayim Minista a tsarin mulkin wasu ƙasashe, kuma ana kallonsa a matsayin matsayi na gaba bayan Sarki a masarautar Hausa.
Saboda haka, kiran Masari da “Waziri” da Tinubu ya yi ya sa mutane da dama suka ɗauka cewa shugaban yana son ƙara nuna masa matsayi da tasiri, musamman kasancewarsa ɗaya daga cikin mutanen da suka fi kusanci da shi a Arewa.
Shi ya sa wasu yanzu suke kiransa “Wazirin Tinubu.”
Wasu na cewa Masari ya yi nasarar tabbatar da cewa ba ƙaramin mutum ba ne a gwamnatin Tinubu, domin ana yawan ganinsa yana gudanar da harkokinsa tare da manyan jami’an gwamnati, gwamnoni da sauran manyan ‘yan siyasa.
Wani mutum da ya yi imanin cewa Masari na da cikakken goyon bayan shugaban ƙasa, amma ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce:
“Duk inda zai je kamfen, gwamnoni, ministoci da manyan jami’an gwamnati suna zuwa tare da shi. Yawanci kuma yana tafiya da dogayen ayarin motoci, tare da motocin wasu manyan jami’an gwamnati da ke raka shi.”
Bincike dai ya gano cewa ana ta raɗe-raɗin cewa Masari shi ne mutumin da wasu ‘yan siyasar Arewa ke ganin ya fi sauƙin kai su wajen neman taimako ko kusanci da Shugaba Tinubu.
Wata majiya ta ce wani gwamna daga Arewa maso Yamma ya taɓa gaya wa wani babban ɗan siyasa cewa ya dace su yi aiki tare da Masari kuma su mutunta ra’ayinsa domin zaman lafiya ya tabbata.
.
Wasu kuma suna ganin ana girmama Masari saboda irin tasirin da ake ganin yana da shi.
Matsayinsa a APC da alaƙarsa da Tinubu
Hawan Masari a cikin APC ya fara bayyana ne ta hanyar rawar da ya taka a tsarin jam’iyyar na ƙasa.
A lokacin Adams Oshiomhole na shugabancin APC, Masari ya taɓa zama National Welfare Secretary na jam’iyyar.
 Wannan ya ba shi damar shiga harkokin cikin gida na jam’iyyar tare da kulla alaƙa da gwamnoni da ‘yan majalisa.
Wannan gogewa ta sa ya zama ɗan siyasar da ya fi karkata ga shirya mutane da harkokin siyasa, maimakon kasancewa kawai mai riƙe da zaɓaɓɓen mukami.
Dangantakarsa da Tinubu ta fara ƙara fitowa fili musamman a lokacin shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A cewar Ahmad Mohammad na Democratic Sustainability Forum, tasirin Masari bai dogara sosai da riƙe zaɓaɓɓen mukami ba ne, sai dai ya samo asali ne daga iya shirya harkokin siyasa, kusanci da shugabannin ƙasa da kuma manyan masu ruwa da tsaki.
Ya ce:
“Masari ya fi fitowa fili wajen ayyukan da ke tallata ajandar siyasar Tinubu da Radda, kuma yana hulɗa da ƙungiyoyi daban-daban a jihohi, ciki har da Katsina.”
Shirye-shiryen zaɓen 2027
Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 suka fara, Masari ya kasance a sahun gaba wajen haɗa shugabannin siyasa a Arewa.
A farkon wannan watan, ya haɗa malamai da malaman addinin Musulunci kimanin 500 daga jihohin Arewa 19 da Abuja (FCT) a Katsina. Bayan taron, aka bayyana cewa mahalarta sun nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
A cikin wata sanarwa daga ofishinsa na yaɗa labarai, Masari ya ce mahalartan sun nuna gamsuwa da abin da suka bayyana a matsayin ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen magance matsalar tsaro da kuma inganta ababen more rayuwa da tattalin arziki a yankin.
Gwamnonin Jigawa Umar Namadi, Kano Abba Yusuf, Yobe Mai Mala Buni, Sokoto Ahmad Aliyu da Kaduna Uba Sani na daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron.
Haka kuma akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin da Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaqa Rabe Darma.
Bayan wannan, Masari ya kuma shirya taron da ya haɗa fiye da malamai 600 na manyan jami’o’in gwamnati a Arewa, inda aka bayyana cewa sun nuna goyon baya ga wa’adin mulki na biyu na Shugaba Tinubu.
Taron ya gudana ne a sirrance a Umaru Musa Yar’adua Centre da ke Kaduna.
A taron akwai Gwamnan Kaduna Uba Sani, Gwamnan Zamfara Dauda Lawal, Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, Gwamnan Borno Babagana Zulum da Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya.
Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Ministan Ƙasa na Tsaro Bello Matawalle, Ministan Gidaje Muttaqa Rabe Darma da tsohon Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari.
Washegari kuma Masari ya gana da mata malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa 19 tare da Gwamnan Kaduna Uba Sani.
A wurin taron, Masari ya tambayi abin da yake ganin shi ne dalilin adawa da Tinubu, yana cewa babban “laifin” shugaban a idanun wasu ‘yan Arewa shi ne kasancewarsa ba Bahaushe ba.
Dangantakar Masari da Radda
Rahotannin bambancin ra’ayi tsakanin Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda da Masari sun jawo hankalin jama’a saboda tarihin siyasar su.
Radda ya samu gagarumar dama a siyasa ne a ƙarƙashin tsohon Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, inda ya taɓa zama Chief of Staff dinsa kafin ya zama shugaban SMEDAN, daga bisani kuma ya lashe zaɓen gwamnan Katsina a 2023.
Ibrahim Kabir Masari kuwa ya ƙara tasirinsa ne ta hanyar tsarin APC da kuma kusancinsa da Tinubu.
Wata majiya da ke kusa da shugabancin APC a jihar ta ce su biyun suna da wuraren tasiri daban-daban amma waɗanda ke iya haɗuwa.
Radda yana da iko a kan gwamnatin jihar da tsarin APC a Katsina, yayin da Masari ke da damar kai tsaye zuwa fadar shugaban ƙasa kuma yana da muhimmiyar rawa a tsarin kamfen na ƙasa.
An kuma samu ce-ce-ku-ce game da zargin lalata allunan tallan siyasa masu ɗauke da hotunan Tinubu da Masari a yankin Modoji Junction zuwa Government House Road a Katsina.
An gayyaci wasu manyan jami’an tsaro da ke aiki tare da Radda zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Abuja domin tambayoyi kan lamarin.
Sai dai majiyar ta jaddada cewa batun allunan tallan kaɗai ba ya tabbatar da cewa akwai rikicin siyasa tsakanin Radda da Masari, domin magoya bayan ɓangarorin biyu sun musanta zargin rashin jituwa.
Wani mai sharhi kan siyasa, Malam Bashir Gambo Matazu, ya ce yanayin siyasar APC a Katsina ya fi rikitarwa fiye da kawai kishiya tsakanin mutane biyu.
Ya ce:
“Dukkan Radda da Masari suna cikin APC kuma suna da alaƙa da shirin sake zaɓen Tinubu. Abin tambaya shi ne ko tsarin tasirinsu daban-daban zai iya tafiya tare ba tare da haifar da bambancin muradu a harkokin jam’iyya, tattara magoya baya da tasiri ba.”
A halin yanzu, babu wata hujja bayyananniya da ke nuna cewa bambancin ra’ayoyin da ake zargi tsakanin mutanen biyu ya rikide zuwa rikicin fili.
Abin da ake iya gani shi ne cewa dukkansu suna iya yin tasiri a lissafin siyasar APC ta hanyoyi daban-daban: Radda a matsayin gwamnan jihar mai ci kuma jagoran jihar, yayin da Masari yake a matsayin mai ba Shugaban Ƙasa shawara kuma mai muhimmiyar rawa a tsarin kamfen na 2027.
Dangantakar Masari da Tinubu ta daɗe
Majiyoyi da dama sun shaida wa Weekend Trust cewa dangantakar Shugaba Tinubu da Ibrahim Kabir Masari ta fara tun kafin burin Tinubu na zama shugaban ƙasa.
Wata majiya daga Katsina ta ce Masari ya fara sanin Tinubu ne ta hannun mutane biyu: Sanata Abu Ibrahim da tsohon Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari.
Tinubu da Abu Ibrahim sun san juna tun lokacin da suka kasance Sanatoci a Jamhuriyar Uku ta Najeriya a 1992. Abu Ibrahim ya wakilci Katsina ta Kudu, yayin da Tinubu ya wakilci Lagos ta Yamma.
Daga baya, dukansu sun bi hanyoyin siyasa daban-daban yayin mulkin soja da kuma dawowar dimokuraɗiyya a 1999.
An ce Abu Ibrahim ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka taka rawa wajen tattaunawar haɗa ƙungiyoyin adawa kafin kafa APC a 2013.
Masari kuwa yana kusa da Abu Ibrahim kuma yana sane da wasu daga cikin waɗannan tattaunawar.
Wata majiya ta ce:
“Kabir Masari ya kasance kusa da Sanata Abu Ibrahim, wanda za a iya kira malaminsa ko ubangidansa a siyasa. Ta wannan hanyar ne ya ƙara kusantar Tinubu.”
Haka kuma, wata hanyar da Masari ya ƙara kusantar Tinubu ita ce ta tsohon Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari.
Aminu Masari, wanda ya taɓa zama Kakakin Majalisar Wakilai daga 2003 zuwa 2007, a yanzu shi ne Shugaban TETFund, mukamin da Tinubu ya naɗa shi.
Daga Nabanje zuwa fadar Shugaban Ƙasa
An haifi Alhaji Ibrahim Kabir Masari kuma ya taso ne a ƙauyen Nabanje, wata ƙaramar al’ummar manoma da ke Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina.
Kamar yawancin yara a ƙauyukan Arewa, rayuwarsa ta farko ta ta’allaka ne kan noma, iyali da rayuwar al’umma.
Ya fara karatun Alƙur’ani a makarantar allo da ke Nabanje kafin ya shiga karatun zamani.
Daga nan ya shiga Fammariya Primary School, inda ya fara karatun boko.
Shugaban makarantar, Malam Yusuf Tanimu, ya bayyana farin cikinsa da yadda Masari bai manta da makarantar da ya fara karatu ba duk da cewa ya kai babban matsayi a siyasa.
An ce makarantar ta samu gagarumin sauyi, ciki har da sabbin kayan ɗaki, ruwan sha da sauran abubuwan da suka inganta yanayin koyarwa da koyo.
Daga Fammariya Primary School, Masari ya wuce Government Day Secondary School, Malumfashi.
Abokan yarinta sun tuna da shi
Shugaban unguwar Nabanje, Alhaji Muhammad Ayuba Umar, ya bayyana Masari a matsayin mutum mai “tsayayyen hali”, yana cewa sun tashi tare tun suna yara.
Ya ce:
“Kabir Masari abokina ne tun muna yara. Mun girma tare kuma har yanzu muna da kusanci. Duk da cewa ya kai babban matsayi, bai manta da tsoffin abokansa ba. Yana taimaka mana kuma bai raina mu saboda matsayinsa ba.”
Alhaji Labiru Musa Kafur, Wazirin Kafur kuma Talban Danejin Katsina, shi ma ya ce ya san Masari tun suna yara.
Ya bayyana Masari a matsayin mutum mai amana kuma mai iya gina gada tsakanin talakawa da gwamnati.
Daga manomi da ɗan kwangila zuwa ɗan siyasa
Kafin ya shahara a siyasa, Masari ya kasance yana harkar noma da kasuwanci tun yana ƙarami.
Haka kuma ya yi shekaru yana harkar gine-gine.
Ɗan’uwansa Muhammadu Sagir Umar Nabanje ya ce Masari ya shiga manyan ayyukan gine-gine, ciki har da gina kusan gidaje 1,000 a Jihar Bauchi.
A cewarsa, wannan sana’ar ta sa Masari ya haɗu da manyan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar, abin da daga baya ya taimaka masa wajen shiga siyasa.
Ɗan’uwansa Haruna Umar Nabanje ya kuma tuna lokacin da Masari ya sayar da gonarsa domin ya samar da kuɗin buga fastoci na wasu ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari.
Ya bayyana shi da kalmar Hausa “Gyare tsohon nama”, wato mutum mai dogon gogewa da juriya a harkokin siyasa.
Taimakon al’umma
An kuma bayyana cewa Masari ya taimaka wa mutane da dama, ba kawai a Nabanje ba har ma a Kafur da sauran sassan Jihar Katsina.
An ce ya tallafa wa ‘yan kasuwa maza da mata da kuɗi da kayan aiki.
Kwanan nan, an ce ya bai wa ɗaruruwan ‘yan kasuwa a Karamar Hukumar Kafur tallafin N300,000 ga kowane mutum.
Mata masu sana’ar yin kuli-kuli da sauran kayan abinci na gargajiya na daga cikin waɗanda suka amfana.
An kuma ce ya taimaka wajen ɗaukar nauyin karatun matasa da dama, tare da tallafa wa ayyukan tituna da sauran abubuwan more rayuwa a yankin.
Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaqa Rabe Darma, wanda ya ce ya san Masari sama da shekaru 25, ya bayyana shi a matsayin mutum mai ɗaukar duk wani nauyi da aka ɗora masa da muhimmanci.
Ya ce irin jajircewar da Masari ya nuna tun zamanin Kungiyar Manoman Arewa, lokacin da marigayi Umaru Musa Yar’Adua yake shugabanta, har yanzu yana nunawa Shugaba Tinubu.
Sanata Ibrahim Ida, wanda ya ce ya san Masari sama da shekaru 30, shi ma ya bayyana shi a matsayin mutum mai son taimaka wa mutane su cimma burinsu.
Ya ce idan Masari yana riƙe da duk abin da yake samu domin kansa, da yanzu ya zama attajiri sosai.
Ci gaban Nabanje
Shugaban unguwar Nabanje kuma kawun Masari, Alhaji Ayuba Umar, ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u sosai.
Ya danganta wasu ayyukan ci gaba a yankin da ƙoƙarin Masari, ciki har da:
Federal College of Agriculture;
hedikwatar ‘yan sanda ta Divisional;
ayyukan hanyoyi;
wutar lantarki mai amfani da hasken rana;
cibiyar Musulunci mai ɗauke da masallaci na zamani;
makaranta;
ɗakin karatu;
gidan limami;
da shaguna.
Wani mazaunin yankin, Malam Ibrahim Shehu Nabanje, ya ce al’ummar sun daɗe suna neman ci gaba, amma yanzu suna iya nuna ayyukan da suka sauya kamannin garin.
An kuma ce sama da ɗalibai 40 da suka kammala karatu sun samu ayyukan yi a matsayin masu kula da gandun daji, yayin da wasu suka samu guraben aiki a hukumomi kamar EFCC da FIRS ta hanyar taimakon Masari.
Wata malamar makarantar Fammariya, Badiya Lawal Gidan Lumo, ta ce hulɗarta da Masari ta nuna mata cewa ba ya nuna bambanci tsakanin addinai. Ta ce ya shiga cikin ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin da ke fama da matsalar tsaro.
Haka kuma, Shugaban Gundumar Kafur, Alhaji Abdulrahman Rabe Abdullahi, ya yaba da irin gudunmawar Masari wajen yaƙi da rashin tsaro, yana cewa ya taimaka wajen ɗaukar matasa aikin sa-kai da kuma samar da kayan tsaro a lokacin da matsalar rashin tsaro ke addabar al’ummomi da manoma.
An kuma bayyana cewa Federal College of Agriculture da ya taimaka wajen samarwa yankin ana sa ran za ta fara gudanar da karatu nan ba da jimawa ba.

About andiya

Check Also

Sanata Aminu Waziri Tambuwal Jagora Ne Abin Koyi –  Atiku Yabo

  Sakamakon irin Nagarta da kokarin aiwatar da ayyuka domin ci gaban  jama’ a yasa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.