Daga Imrana Abdullahi
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa da sauran al’amuran Alhaji Ibrahim Kabir Masari, tare da ministan ma’aikatar gidaje Injiniya Muttaqha Rabe Darma sun kai ziyarar gaisuwar Ta’aziyya ga Dokta Hakeem- Baba- Ahmed Sakamakon rasuwar dan uwansa Malam Nafi’u Baba- Ahmed wanda ya kasance sakatare janar na majalisar kula da harkokin Shari’a a Najeriya (SCSN).
Alhaji Ibrahim Kabir Masari wanda ya kasance jagoran tawagar manyan mutanen da suka kai gaisuwar Ta’aziyyar ga Baba Ahmed sun jajantawa iyalan Marigayin tare da yi mashi addu’ar neman gafarar Ubangiji.
Wadanda suka kasance a cikin tawagar sun hada da minista Muttaqha Rabe Dama, kodinetan shirin NEPAD Jabiru Abdullahi Tsauri, Shaikh Abu Ammar,Honarabul Aminu Tukur da dai sauran muhimman mutane da dama da ke cikin tawagar.
A yayin ziyarar, Shaikh Abu Ammar ya gabatar da yin addu’a ga mamamcin inda ya roki Allah da ya gafarta masa dukkan kurakuransa ya kuma karbi ayyukansa da ya yi masu kyau ya saka masa da gidan Aljanna maɗaukaki ya.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba iyalan Marigayin, yan uwa da dukkan abokan arzikin hakuri jure rashin.
THESHIELD Garkuwa