Home / Labarai / Muna Taimakawa Al’umma Ne – Minista Muttaqha Darma

Muna Taimakawa Al’umma Ne – Minista Muttaqha Darma

 

Daga Imrana Abdullahi

 

 

 

.Ministan ma’aikatar Gidaje da bunkasa yankunan karkara na Tarayyar Najeriya Injiniya Muttaqha Rabe Darma, ya bayyana cewa dukkan abubuwan da yake yi duk domin taimakawa al’umma ne ta yadda mafi yawa daga ciki za su gamsu.

Ministan ya ce hakika ko a yanzu jama’ar suna ta gamsuwa sakamakon ci gaban da suke za mu ta fuskara irin abubuwan da ake yi.

“Muna yi wa Allah madaukakin Sarki godiya ko a yanzu mutane sun karbi duk abin da ake yi da hannu biyu biyu kuma mu tsakanin mu da Allah muna yi ne domin taimakawa al’umma”.

Amma ya kara da cewa duk da hidima ga al’umma abu ne mai wahala amma a koda yaushe ya na yin kokarin ganin ya hidimtawa jama’ar domin taimako saboda Allah madaukakin Sarki, don haka za mu kara kokarin yin abin da muke aikata wa.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka Yayin Da Zamfara Ke Cika Shekaru 30

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.