…Fatan mu Shi ne Atiku Ya zama shugaban ƙasa – Shugaban Atiku Global Concept,mobilization
Daga Imrana Abdullahi
An bayyana tafiyar goyon bayan Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya a matsayin tafiya domin ceton kasa tare da al’ ummar ta baki daya.
Shugaban wata hadaddiyar kungiyar da ke fafutukar ganin Alhaji Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa a Tarayyar Najeriya Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana hakan a wajen taron kungiyar da ya gudana a Kaduna.
“Alhaji Atiku Abubakar Global Concept and Mobilization kungiya ce mai rijistar kamar yadda dokar kasa ta bayar da dama, don haka ba mu da wata manufa sai ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya samu nasara a zaben shekarar 2027 da za a yi, saboda haka muke yin kira ga xaukacin jama’a da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga wannan tafiyar.
Tafiya ce ta ceto Nigeria duk jam’iyyar da mutum yake yi ya tabbatar da Atiku ne shugaban kasa.
“A Watan Mayu 2027 za a tabbatar an zabi Atiku Abubakar ya lashe zabe a kori annobar da ke damun Najeriya a matsayin ƙasa mai yancin gashin kanta.
Wadansu mutane irin su Patrick Lumumba da dai sauran wasu jagorori a Afirka, da kuma Nigeriya
.Da ikon Allah sai mun kafa Atiku ya zama shugaban ƙasa domin duk abin da za a yi hadin ne kawai z a yi
” Ta yadda yaya da jikoki za su samu abin da ya dace ba kamar yadda ake ciki a halin yanzu ba don haka ne za mu dauki Wazirin Adamawa ya zama shugaban kasa.
Za a yi wannan fafutuka ne a matsayin mataki mataki tun daga Unguwanni, Mazauni,Kananan hukumomi zuwa jiha da kasa baki daya.
” Ko ba ku san Atiku ba to lallai ku zabe shi domin ya na da aniyar mai kyau.
“Mun zauna da Atiku Abubakar ya yi murna ya amshi wannan kokarin na mu da muke yi a halin yanzu don haka ba zamu ba shi kunya ba ba za mu ba Talakawa kunya ba tafiya ce kawai ta zama shugaban ƙasa .
Daga wannan kokarin sai kuma aiki na biyu da zarar ya fara Kamfe za mu ta fi jihar da zai je kafin lokacin da zai je Jihar sannan ya je jihar.
Za mu yi amfani da gidajen rediyo a ƙalla mu yi shirin tattaunawa na akalla mintinan 30 mu fadi abin da ya sa za a zabi Atiku Abubakar.
“Ni a matsayin na na dan APC na zan ci amanar yankin arewa ba da al’umma ta ba, don haka a ranar 18 ga wannan watan za mu fara wannan aikin zai kuma a fara aikin ne da Jihar Kano.
“Kuma wannan tafiya ce a bude yadda kowa zai san abin da ke faruwa abin da ake yi.
Muna da kwamitoci kamar haka
1- Publicity Commity
2- Security
3- Logistics
4- Medical team
5- Contacts and mobilization
Honarabul Sa’idu Usman Gombe, da takarar majalisar dokokin jihar Kaduna daga gundumar Kawo Kaduna,ya ce Daman shi ya kirkiro da tafiyar sai ya kawo Ni cikin ta na kuma rungume ta domin muhimmancin ta.
” Kamar yadda aka gabatar da wannan tafiya mun yi tafiya kamar irin wannan a can baya, na ci karo da shi ne sakamakon irin yadda yake fadin ra’ayinsa
Kuma kamar yadda na fahimce shi kishi ne ya sa ya dawo daga waccan tafiyar duk da suna da abin duniya.
“Matsalar cire tallafi mai ne mu sababbin. shigar Najeriya cikin halin da ake ciki a halin yanzu, lamarin da ya haifar da shigar kasa da yan kasa cikin tsadar rayuwa.
Shi ya sa muke cewa mu ajiye bambancin siyasa mu yi koyi da abubuwan da magabatan Arewa suka yi na sadaukar wa har muka samu kan mu a halin yanzu.
“Akwai wadansu ma’aukatun Gwamnati an kwashe daga arewa an mayar da shi kudancin Najeriya.
Idan za ayi Gwagwarmaya sai an cire duk wani bambanci domin a samu ci gaban kasa da al’ummar ta.
“Ni dan takarar ne a PDP amma ina gaya wa mutane cewa zan zabi Atiku ne kuma duk wanda zan gaya wa ya zabi shugaban kasa zan ce ya zabi Atiku Abubakar ne domin ba zan iya fadin sunan dan takarar shugaban kasa na PDP ba”.
Ambasada Danjuma Idris Sani tsohon kadan Najeriya a kasar Misra, kira ya yi ga al’umma da su dukufa wajen yin addu’a domin samun nasara, domin halin da ake ciki akwai matsala a fannin gudanar da zaben Najeriya kamar yadda muke gani ana zargin kamar ba za a yi zabe ba.
Mutane da dama a wajen taron sun tofa albarkacin bakinsu game da tafiyar Atiku Abubakar a zaben shekarar 2027 da ake bukatar sai kowa ya shirya tsaf.
THESHIELD Garkuwa