Home / Labarai / Tinubu Ya Dakatar Da  Emefiele A Matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN

Tinubu Ya Dakatar Da  Emefiele A Matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN

Daga Imrana Abdullahi

Bayanan da suke fitowa daga ofishin sakataren Gwamnatin Najeriya na cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, CFR daga aiki ba tare da bata lokaci ba.

Bauanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar a yammacin ranar Juma’a.

Daga Imrana Abdullahi

A cewar sanarwar, dakatarwar “ta biyo bayan binciken da ake yi ne a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar.

“Sabarwar ta ce an umurci Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamna mai kula da Ayyuka,

Mista Folashodun Adebisi Shonubi, wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar, har sai an kammala bincike da kuma gyara.”

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.