Home / Labarai / An Daɗe Da Dakatar Da ’Yan Majalisa 8 Da Suka Sauya Sheƙa – Kakakin Majalisar Zamfara

An Daɗe Da Dakatar Da ’Yan Majalisa 8 Da Suka Sauya Sheƙa – Kakakin Majalisar Zamfara

 

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Ismail Moriki, ya bayyana cewa ’yan majalisa takwas da suka sanar da ficewarsu daga Jam’iyyar APC kwanan nan, an dakatar da su daga majalisar tun kafin sanarwar sauya sheƙarsu.

Kakakin ya ce Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da ’yan majalisar ne tun ranar 26 ga Fabrairu, 2024, bisa zarge-zargen aikata munanan laifuka, haɗa baki, tada zaune tsaye, raina majalisa da kuma shirya zaman majalisa ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya saɓa wa dokokin gudanar da ayyukan majalisar.

A cewar majalisar, zarge-zargen da ake yi wa ’yan majalisar sun wuce batun karya ƙa’idojin gudanar da majalisa kawai.

An zarge su da aikata abubuwan da suka yi kama da kutsen gida, shiga ofisoshi da ƙarfi da kuma lalata dukiyoyin gwamnati, ciki har da zargin daƙile ƙofofin ofisoshin Magatakardar Majalisa da Jami’in Tsaron Majalisa, tare da yin amfani da ƙarfi wajen shiga zauren majalisar.

Haka kuma, an zarge su da lalata wasu kadarorin majalisar, kafin daga bisani su gudanar da wani zaman majalisa ba tare da izini ba.

Muhimmancin zarge-zargen ya sa daga bisani aka shigar da ƙarar laifi a kan ’yan majalisar da aka dakatar a gaban kotun da ke da hurumin sauraron irin wannan ƙara.

Da yake martani kan sanarwar da suka yi ta ficewa daga APC, Kakakin Majalisar, Moriki, ya ce matakin nasu wata hanya ce ta karkatar da hankalin jama’a daga ainihin batutuwan ladabtarwa da suka jawo dakatar da su, tare da ƙoƙarin haifar da tunanin cewa Majalisar Dokokin Jihar Zamfara na cikin rikici.

Ya ce Majalisar Dokokin Jihar Zamfara tana cikin kwanciyar hankali, tana aiki yadda ya kamata, kuma tana ci gaba da gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora mata.

“Majalisar Dokokin Jihar Zamfara tana cikin kwanciyar hankali, tana aiki yadda ya kamata kuma tana ci gaba da gudanar da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata. Ba za a iya gabatar da sauya sheƙar ’yan majalisar da aka dakatar ba a matsayin hujjar cewa majalisar na cikin rudani.

“An dakatar da waɗannan ’yan majalisa ne bisa zarge-zargen aikata munanan laifuka da kuma take wasu muhimman dokokin gudanar da majalisar, ciki har da zarge-zargen shiga ofisoshin majalisar da ƙarfi, lalata dukiyar gwamnati da gudanar da zaman majalisa ba tare da izini ba.

“Saboda haka, dakatar da su ba ta da alaƙa da matakin siyasar da suka ɗauka yanzu. Dakatarwar ta faru tun kafin sanarwar sauya sheƙarsu, kuma ta samo asali ne daga batutuwan ladabtarwa da suka shafi majalisar,” in ji Moriki.

Kakakin ya ƙara bayyana cewa a ranar 13 ga Mayu, 2026, Majalisar ta amince da tsawaita dakatarwar ’yan majalisar zuwa wani ƙarin zangon majalisa, sakamakon rashin warware batutuwan ladabtarwa da kuma take dokokin majalisar.

Ya ce wasu ’yan majalisa biyu da aka dakatar a baya sun nemi afuwar majalisar, daga bisani aka mayar da su bakin aiki, abin da ya ce ya nuna cewa matakan ladabtarwar ba na siyasa ba ne, kuma ba a ɗauke su ne domin muzgunawa wata jam’iyyar siyasa ba.

Moriki ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ba ta da ƙarfin gudanar da ayyukanta, yana mai cewa a halin yanzu majalisar na da ’yan majalisa 16 da ke gudanar da ayyukansu, kuma tana ci gaba da zaman majalisa bisa tanadin kundin tsarin mulki da dokokin gudanar da majalisar.

“Majalisar ta gudanar da zaman cikakken zaurenta a ranar Talatar da ta gabata, kuma an tsara ta sake zama gobe, Litinin. Saboda haka, babu wani dalili ko kaɗan na bayyana Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a matsayin majalisar da ke cikin rudani,” in ji Kakakin.

Ya buƙaci jama’a su bambanta tsakanin shawarar siyasar da ’yan majalisar da aka dakatar suka ɗauka da kuma matakan ladabtarwa da aka daɗe ana ɗauka a kansu.

Ya ce sauya jam’iyyar siyasa ba ya soke ko kawar da batutuwan ladabtarwa da suka shafi majalisa, haka kuma ba ya rusa shari’o’in da ke gaban kotu da suka samo asali daga zarge-zargen aikata ba daidai ba.

Kakakin ya sake jaddada aniyar shugabanci da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara wajen kare bin doka da oda, mutuncin majalisar da kuma kare cibiyoyin gwamnati da dukiyoyin jama’a.

About andiya

Check Also

JIHAR ZAMFARA A Shekaru 30: Yau Jiragen Sama Na Kasuwanci Suka Fara Zirga-zirga, Abuja Zuwa Gusau

A yau ne za a fara jigilar jirgin saman kasuwanci na farko tsakanin Abuja da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.