Home / KUNGIYOYI / Kungiyar ta yi Allah-wadai da juyin mulkin Nijar

Kungiyar ta yi Allah-wadai da juyin mulkin Nijar

….da kiraye-kirayen shiga tsakani daga waje

Daga Imrana Abdullahi

Kungiyar kawancen Najeriya da Nijar a ranar Juma’a ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar tare da yin kira da a tsoma bakin kungiyoyin kwadago a Afirka.

Malam Ahmad Altine, shugaban kungiyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce: “Kungiyarmu ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.

“Muna kira ga Kungiyar Tarayyar Afirka da Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) da kuma Majalisar Dinkin Duniya da su matsa lamba kan gwamnatin mulkin sojan da ta gaggauta maido da mulkin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar.”

Shugaban  ya ce kungiyar ta jajantawa iyalan  Shugaban kasa Muhammad Bazoum saboda irin halin da suke ciki a halin yanzu.

Altine ya yi kira ga dukkanin kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar da su yi tir da juyin mulkin.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Refutes False Claims on PMS Export and Re-importation

    The Management of Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals has noted with concern the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.