Home / Labarai / Ina Goyon Bayan Palastinawa – Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi

Ina Goyon Bayan Palastinawa – Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi

Daga Imrana Abdullahi
Dokta  Sulaiman Shuaibu Shinkafi, sanannen dan Gwagwarmaya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga  Kasar Palasdinu da al’ummar Palasdinawa, inda ya kafa tutar kasar Palasdinu a gidansa da ke unguwar Badarawa cikin garin Kaduna da ke arewacin tarayyar Najeriya.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya kuma yi kira ga daukacin manyan kasashen duniya da suka hada da Najeriya da su taimakawa kasar Palasdinu da Palastinawa da addu’a su samu zaman lafiya da nufin Allah ta’ala ya yaye masu masifar da suke ciki.
#muna goyon bayan Palasdinawa🇵🇸

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.