Home / Labarai / Mutane Biyu Masu Dauke Da Cutar Covid- 19 Sun Tsere A Jihar Barno

Mutane Biyu Masu Dauke Da Cutar Covid- 19 Sun Tsere A Jihar Barno

 

Kamar yadda muke samun wadansu ingantattun rahotonnin daga jihar Borno, sun tabbatar da cewa mutane biyu sun gudu da ke jinya dauke da cutar Covid – 19  a jihar, kamar yadda kafar yada labarai ta TheCable ta ruwaito.

Mutum biyun sun gudu ne bayan gwajin da hukumar kula da Lafiya ta NCDC ta yi masu ya na tabbatar da suna  kamu da cutar, inji Kwamishinan lafiya na jihar Salish kwayabura.

Kwamishinan yace ana zargin Abba Kaka Hassan mai shekaru 24, tare Hauwa Mohammed mai shekaru 42, da tserewa daga asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, bayan an tabbatar da suna dauke da cutar.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.