Home / Big News / Kungiyar Zabi Sonka Ta Kasa Reshen Jihar Kaduna Sun Kaddamar Da Kalanda

Kungiyar Zabi Sonka Ta Kasa Reshen Jihar Kaduna Sun Kaddamar Da Kalanda

 

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an kara karfafa dankon zumunci a tsakanin al’ummar tarayyar Najeriya da kuma jama’ar wadansu kasashe kungiyar Zabi Sonka ta kasa reshen Jihar Kaduna sun kaddamar da kalandar da ke dauke da hotunan ya’yan kungiyar, sarakuna da kuma shugabannin al’umma daban daban.
Alhaji Sallau Dan mato Tokarawa kenan a lokacin da yake kaddamar da kalandar a wajen taron, ya dai halarci taron ne daga Nijar Kano
Alhaji Danjuma Furana tare tare da dimbin ya’yan kungiyar sun bayyana gamsuwa da irin kwazo tare da hadin kan da ya’yan kungiyar suka bayar wajen ciyar da kungiyar da kasa gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Alhaji Sallau Dan mato Tokarawa daga jihar Kano ya bayyana irin wannan kokarin na samar da Kalandar kungiya a matsayin wani babban al’amarin da kowa zai yi alfahari da shi.
Wasu daga cikin ya’yan kungiyar zabi Sonka a Jihar Kaduna kenan suke tattaunawa a kan yadda kalandar ta yi kyau
An dai yi taron ne a harabar gidan rediyon Quen FM da ke garin Zariya, taron dai ya samu halartar dimbin ya’yan kungiyar daga ciki da wajen Jihar Kaduna

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.