Home / Labarai / RIKICIN ZAƁEN ƊAN TAKARAR GWAMNAN JIHAR KADUNA

RIKICIN ZAƁEN ƊAN TAKARAR GWAMNAN JIHAR KADUNA

SANARWAR MANEMA LABARAI

 

23 ga Yuli, 2026

 

 

 

 

A ranar Talata, 21 ga Yuli, 2026, wasu zaɓaɓɓun mambobin Kwamitin gudanarwa na Jiha (SWC), tare da shugaban karamar hukuma guda ɗaya da shugaban mazabar Kwarbai “B”, sun gudanar da zama a Abuja domin tattauna rikicin siyasa da ya dabaibaye jam’iyyarmu a Jihar Kaduna, musamman yunƙurin da ake yi na ɗora Barista Mohammed Sani Abbas a matsayin ɗan takarar gwamna, alhali ba a gudanar da zaɓen fidda gwani ba a ranar 29 ga Mayu.

Domin fayyace gaskiya, zaɓen fidda gwani na gwamnan Jihar Kaduna bai gudana ba a ranar 29 ga Mayu. Hakan ya biyo bayan umarnin shugaban kwamitin zaɓe na NDC na jihar Kaduna, Farfesa Silva Opuala-Charles, wanda ya umarci shugaban Jam’iyyar na jiha da ya gayyaci duk masu neman takarar gwamna domin a yi ƙoƙarin cimma matsaya ta yarjejeniya (Consensus).

Kwamitin zaɓe, SWC da masu neman takarar sun shafe tsawon ranar suna tattaunawa domin cimma matsaya wadda za ta samar da halastaccen ɗan takara. Sai dai ba a cimma wata yarjejeniya ba, don haka zaɓen fidda gwani da aka tsara gudanarwa a ranar 29 ga Mayu bai gudana ba, kuma har zuwa yau ba a gudanar da shi ba.

Haka kuma, a wancan lokaci ba a cimma yarjejeniya tsakanin masu neman takara uku ba, wato: Ibrahim Hussaini Abdulkarim
Zariyi Yusuf Madaki
Mohammed Sani Abbas

Daga baya kuma Sanata Danjuma La’ah ya shiga jam’iyyar tare da bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamna, wanda ya ƙara yawan masu neman takarar zuwa huɗu.

AN ƊORA ƊAN TAKARA BA TARE DA BIN DOKA BA

Abin mamaki, ba tare da gudanar da zaɓen fidda gwani ko cimma yarjejeniya ba, Sanata Danjuma La’ah ya bayyana a gaban kwamitin gudanarwa na Jiha (SWC) dauke da fom ɗin takara da kuma shaidar biyan Naira miliyan 30 na fom ɗin nuna sha’awa da fom ɗin takara. Ya bayyana wa SWC cewa sakataren jam’iyya na kasa ne ya ba shi fom ɗin takarar gwamna tun ranar 25 ga Mayu, kwanaki huɗu kafin ranar da aka tsara gudanar da zaɓen fidda gwani.

JIHAR KADUNA TA ƘI AMINCEWA DA ƊORA ƊAN TAKARA

Muna sanar da jama’a cewa an ɗora Mohammed Sani Abbas a matsayin ɗan takarar gwamna ba tare da bin tsarin doka ba.

Da Barista Mohammed Sani Abbas da kuma Sanata Danjuma La’ah basu sami zama yan takaran jimma’iyan NDC ba domin basu fito daga zaben fidda gwani ta NDC ba. Ba ingantacciyar hanyar da Sashe na 87 (1–3) na Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada ba kenan.

Dokar ta tanadi cewa:

Idan jam’iyya za ta zaɓi ɗan takara ta hanyar yarjejeniya, dole ne duk waɗanda aka tantance su rubuta amincewarsu tare da janye takararsu da kuma amincewa da ɗan takarar da aka zaɓa.
Idan ba a samu wannan cikakkiyar amincewa ba, dole ne jam’iyyar ta koma tsarin zaɓen fidda gwani kai tsaye (Direct Primary).
Bayan yarjejeniya, dole ne a gudanar da taron amincewa (Convention ko Nomination Congress) kamar yadda doka ta tanada.

ABIN DA MUKE NEMA

Abin da muke nema yana da sauƙi. Muna kira ga shugabancin jam’iyyar da su shirya gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani, ko dai ta hanyar yarjejeniya bisa doka ko kuma ta hanyar zaɓen fidda gwani kai tsaye, domin a samu halastaccen ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna da ya fito bisa tsarin doka.

KIRANMU NA NEMAN ADALCI

Mambobin NDC na jihar Kaduna na fuskantar barazanar hana su haƙƙinsu na kundin tsarin mulki na zaɓar wanda zai wakilce su.

Muna Allah wadai da duk wani yunƙuri na ɗora ɗan takara ta hanyar da ba ta dace da dimokuraɗiyya ba.

Abin da ya faru a Abuja ba sulhu ba ne, ba yarjejeniya ba ce, kuma ba zaɓen fidda gwani kai tsaye ba ne. Wannan mataki ya saɓa wa Sashe na 87 (1–3) na Dokar Zaɓe ta 2026.

MUNA KIRA DA A WARWARE RIKICIN CIKIN ADALCI, LAFIYA DA BIN DOKA

NDC ta Jihar Kaduna tana kira ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa da su tabbatar an bi tsarin dimokuraɗiyya wajen zaɓen ɗan takarar gwamna kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.

Dokar ta ba mambobin NDC na Jihar Kaduna kaɗai ikon zaɓar ɗan takarar gwamna.

Haka kuma Sashe na 36 na Dokar Zaɓe ta 2026 ya ba INEC damar tsawaita lokacin karɓar sunayen ‘yan takara idan wata jiha ta kasa samar da halastaccen ɗan takara.

Dokar ta ce:

“Idan lokacin karɓar sunayen ‘yan takara ya ƙare ba tare da samun halastaccen ɗan takara ba, Hukumar Zaɓe za ta tsawaita lokacin karɓar sunayen tare da sanya sabon ranar zaɓe.”

Muna fatan shugabancin jam’iyyar na ƙasa ba zai ɗauki wani mataki da zai hana Jihar Kaduna samun damar tsayar da halastaccen ɗan takara ba.

Duk wani yunƙurin tura sunan ɗan takara wanda bai fito ta hanyar yarjejeniya ta doka ko zaɓen fidda gwani da INEC ta sa ido a kai ba, zai hana Jihar Kaduna samun halastaccen ɗan takara wanda INEC da mafi yawan mambobin NDC za su amince da shi.

SHAWARARMU

Muna ba shugabancin jam’iyyar na ƙasa shawara da su yi amfani da tanadin Sashe na 36 na Dokar Zaɓe ta 2026 su rubuta wa INEC domin ta sanya ido kan sabon zaɓen fidda gwani ko tsarin yarjejeniya, ta yadda za a samar da halastaccen ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna wanda mafi yawan mambobin jam’iyya za su amince da shi.

Duk wani mataki da ya saɓa da wannan ba zai amfani jam’iyyar NDC ta Jihar Kaduna ba.

 

Sa hannu

Isaac Dambvou Tanko
Sakataren Yaɗa Labarai na NDC, Jihar Kaduna

About andiya

Check Also

Gwamna Uba Sani Ya Raba wa Mutanen Alhuhuda Filayen 92 A Zariya

  Daga Imrana Abdullahi A wani babban taron da aka yi a dakin taron makarantar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.