Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga cikin garin Katsina na bayanin cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina kuma ɗan takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar ADC Alhaji Dokta Mustapha Muhammad Inuwa ya fice daga ADC ya koma APC inda zai yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda tare da shugaba Tinubu yakin neman zabe a shekarar 2027.
Dokta Mustapha Inuwa Ya shaidawa manema labarai a Katsina cewa ya dauki wannan matakin ne Bayan tattaunawa da ya yi da jama’arsa da wasu ma suka kafata a fice daga ADC domin an ki yin zaben fidda dan takarar gwamna.
“Duk da mun shiga APC dole za mu ci gaba da fadin gaskiya idan an yi abin da ke bukatar hakan domin ba za mu yi shuru ba kuma Daman a irin wadannan kafafen ne muke samun damar aikawa da gwamnati duk wani sako, amma a yanzu tun da ga mu ga su ai shikenan ba wata matsalar da za a samu ta bayyana abin da ya kamata domin Ni da shi Gwamnan a wani zaman da muka yi sai da na gaya masa cewa ya bayar da dama a rika gaya masa gaskiya.
“Ina mutum zai koma dole sai dai APC takamata jam’iyya mai rogo ko ADC da na ta ma a cikin dokar kasa domin kotun daukaka kara ta ce babu ita kamar yadda ta yanke hukunci.
Za kuma mu tabbatar an samu cimma ga ci a koda yaushe.
THESHIELD Garkuwa