Daga Imrana Abdullahi
Bayanan Da muke samu a cikin sanarwar da Gwamnati ta fitar na jerin sunayen masu yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yakin neman zabe na tabbatar da cewa ministan kula da ma’aikatar gidaje da raya yankunan karkara Injiniya Muttaqha Rabe Darma ne zai yi wa kwamitin aiki a matsayin Daraktan fadakarwa wato Darkta Mobilization a Shiyyar arewa maso Yamma duk da nufin samun gagarumar nasarar da ake bukatar samu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Al’ummar Jihar Katsina da arewacin Najeriya dai minista Darma lallai ba bakonsu ba ne kasancewar ministan mutum ne da aka san shi wajen jibantar al’amuran da suka shafi jama’a.
Ana yi wa minista Muttaqha Rabe Darma fatan alkairi.
THESHIELD Garkuwa