Related Articles
Daga Imran a Abdullahi
Bayanan Da muke samu daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na cewa an nada Samata Abdul’aziz Abubakar Yari a matsayin babban Daraktan Janar na shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tunkarar zaben shekarar 2027 mai zuwa.
An kuma ruwaito cewa an bayyana sunan Sanata Adam Oshiomhole a matsayin mataimakin darakta Janar na yakin Neman zaben da zai yi aiki a matsayin mai fadakarwa da wayar da kan jama’a a kamfen din.
Yayin da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Gbajabiamila zai yi aiki a matsayin darakta janar mai kula da harkokin mulki.
An kuma tabbatar da Gwamna Hope Uzodimma a matsayin sakataren Kamfe din,sai kuma sakataren jam’iyyar APC na kasa Santa Ajibola Bashiru da Hadiza Bala – Usman za su yi aiki a matsayin mataimaki da mai taimakawa sakatariyar tafiyar.
THESHIELD Garkuwa