…Tafiya ta Waziri ce komai nawa Waziri ne kawai a cikin kowace kwarkwada – kwarkwada a koda yaushe
Daga Imran a Abdullahi
Shugaban kungiyar Alhaji Atiku Abubakar Global Concept Mobilization, 2027 Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana cewa babban burin su kawai shi ne Atiku ya zama shugaban kasa a zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Suleiman Shinkafi ya bayyana hakan ne. Lokacin da ya karbi baƙuncin jagororin tallar Atiku Abubakar, Maza da Mata daga karamar hukumar Igabi da Unguwar Shanu cikin karamar hukumar Kaduna ta arewa a cikin Jihar Kaduna da suke fafutukar ganin da ikon Allah sai Atiku ya zama shugaban kasa.
Matsalar rashin tsaro ta tagayya jihar Zamfara duk da cewa a yankin arewa maso Yamma babu jihar da Bola Tunubu ya lashe zabe sai Zamfara.
“Mun samu tabarbarewar tattalin arzikin jama’a a jihar Zamfara duk da irin kuri’ar da muka ba
Saboda kishin al’umma da kishin kasa ya sa Ni a matsayina na wanda ke tare da Ministan tsaro na ce ba zan yi tallar Tunubu ba ko kadan, babban dalilin mu a nan shi ne a wancan karon mun zuba dukiyar mu na raba mota 47 ga jama’a na raba na’ura mai ƙwaƙwalwa da yawa da sauran kaya da yawa ga jama’a duk domin ganin Tunubu ya lashe zabe kuma ya yi samu nasara amma mu a jihar Zamfara kun koma koma baya a cikin kasa.
Don haka ina kira gare ku lallai ku yi amfani da kuri’arku ku zabi Atiku Abubakar, domin shi ne mafita.
“Ni dan jam’iyyar APC ne amma ba zan yi tallar Tunubu ba, tallar Atiku zan yi saboda shi nake ganin wanda zai lashe zabe ya kawo wa kasa ci gaba da al’ummar ta baki daya.
“Za mu kunna Lasifika mu ba jama’a a ko’ina ,muna cewa Yan Arewa Ku farka kada ku yi zaben tumun Dare ku zabi cancanta kuma wanda ya cancanta shi ne wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar.
“Sai dai mu ba za mu yi SAK ba, amma kuma sane cewa gwamnatin Atiku matasa zai zuba wadanda sune mutanen gaskiya da ci gaban kasa baki daya.
“Jama’a ya dace ku farka domin fita daga cikin halin da ake ciki, da an yi mana adalci za mu yi Tunubu amma tun da a yanzu bakin alkalami ya bushe ba a yi mana adalci ba. Duk wanda ya bar Atiku ya zabi wani can daban to a duba kwakwalwar sa domin akwai wani abu daban.
“Mu ba bayi Ba ne tuni an daina yin bautar bayi,ko ba ko sisi za mu yi Atiku.
Muna yin wannan aikin ne a karkashin Kungiya mai suna Alhaji Atiku Global Concept Mobilization 2027
Musa Dauda Dan Mani, cewa ya yi tallar Atiku Abubakar tallarsa ta riga ta karbu sai dai kawai ranar zabe.
Sai ya ci gaba da cewa babban aikin su a nan shi ne yaya za a kare kuri’a a ranar zabe domin za a fafafta ne da jam’iyyar APC da daukacin Yan Najeriya da suke cikin wani mawuyacin hali.
” Ga mata Nan da su ne ke dauke da wahalhalun gida a ƙalla kashi Tamanin (80) don haka a yi kokari mata a san abin da ya da ce, mun ci zabe idan Allah ya amince sai dai kare kuri’a kawai.
Hadiza Ibrahim daga Unguwar Rigasa karamar hukumar Igabi dalilin zuwan mu wannan wurin sai domin yin aikin ceton al’umma ta hanyar zaben Atiku Abubakar.
“Akwati dari da wani abu a unguwar Rigasa duk za mu lashe zabe a ranar zabe, domin a yanzu kishin Dan Arewa kawai ake yi domin a fita daga halin da ake ciki.

Kungiyar Youth Mobilization for Atiku 2027 sun kawo ma Dokta Suleiman Shinkafi ziyara da nufin hadewa tare da kungiyar Alhaji Atiku Abubakar Global Concept Mobilization, 2027
Inda suka bayar da shawara cewa ya na da kyau ayi wani horo ga wadanda za a ba Ladifikikin da za su yi amfani da su domin a horar da su a kan abin da za su fadi a cikin al’umma.
THESHIELD Garkuwa