Daga Imrana Abdullahi
Dan majalisa wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Bungudu da Maru da ke Jihar Zamfara, Honarabul Abdulmalik Zubairu Zannah ya taimaka da motoci 15 ga ofishin yakin meman zabe na Tinubu da Gwamna Dauda Lawal.
An dai bayar da wadannan motocin ne ga kungiyar APC Daram Dam Dan domin yin aiki ta yadda za a samu nasarar zaben 2027 mai zuwa.
Wadanda za su amfana da wannan taimakon motocin sun hada da shugabannin wannan ƙungiya a dukkan kananan hukumomi Goma sha hudu (14) da ke jihar
Gwamna Dauda wanda ya mika motocin ga wadanda suka amfana ya shawarce su da su yi amfani da motocin kamar yadda ya dace domin nasarar APC.
Gwamnan wanda kwamishinan kula da ma’aikatar kananan hukumomi da masarautar gargajiya Ahmad Yanzu, ya wakilta bayyana wannan kokari ya yi na dan majalisar da irin yadda yake son ganin an samu nasara da kuma taimakawa matakan yakin neman zabe da suke a can kasa tun daga masani.
Gwamna Dauda ya kuma yabawa dan majalisar bisa irin wannan namijin kokarin da ya yi domin taimakawa jam’iyyar APC a jihar Zamfara baki daya, da haka ne Gwamnan ya yi kira ga sauran jam’iyya da su yi ko yi da abin da dan majalisar ya yi.
Wannan tallafin motocin zai taimakawa yakin neman zaben APC ayi shi zuwa lungu da sakon na jihar.
Gwamna Lawal ya kuma shawarci ya’yan jam’iyyar APC da kuma baki dayan masu ruwa da tsaki a cikin jihar da su kara matsa kaimi domin samun nasarar Bola Tinubu da Dauda lawal tareda dukkan yan takarar APC a kowa ne mataki.
Da yake gabatar da jawabi, Alhaji Bashir Bello Auki, wanda ya wakilci dan majalisa Sannan,cewa ya yi wadannan motocin an samar da su ne domin gudanar da yakin neman zaben Tinubu /shattima da kuma Gwamna Dauda kawai da nufin a sake zaben su karo na biyu tare da dukkan sauran yan takarar APC a fadin Jihar Zamfara.
Ya bayyana cewa su shugabannin sune za su tafiyar da yakin neman zabe a mazauni 147 da ke Jihar Zamfara,saboda da haka ne ake kan hankalinsu da su yi amfani da motocin ta hanyar da ya dace.
Shugaba na jiha da ke fafutuka a kan ganin jam’iyyar APC ta kara darewa kan karagar mulki da ake kira APC Daram, Dam Dam, Alhaji Shamsu Kasida ya bayyana wannan samar masu da motocin aiki da cewa wani babban lamari ne da ke karfafa Gwiwa a samar masu da motocin aiki.
THESHIELD Garkuwa