Home / Labarai / An Kira Maniyyatan Hajiin Bana Na Shiyyar Funtuwa, Dutsinma

An Kira Maniyyatan Hajiin Bana Na Shiyyar Funtuwa, Dutsinma

IMRANA ABDULLAHI
BAYANAN da muke samu daga hukumar Alhazai ta Jihar Katsina na cewa hukumar ta kira ragowar Maniyyatan kananan hukumomin yankin Funtuwa da kuma wasu daga Dustinma da su hallara a sansanin Alhazai da ke kan hanyar Daura a Katsina domin shirye shiryen tafiya kasa mai tsarki su sauke farali.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar jin dadin Alhazan Jihar Katsina Badaru Bello Karofi.
Sai kuma Maniyyatan shiyyar Dutsinma da kuma kananan hukumomin Batagarawa, Charanchi sai Alhazan karamar hukumar Jibiya na shekarar 2020 kawai da su hallara a sansanin Alhazan.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.