Home / Labarai / Shugaba Bola Tinubu Na Yin Gyara Ne A Najeriya – Dokta Muttaqha Rabe Darma 

Shugaba Bola Tinubu Na Yin Gyara Ne A Najeriya – Dokta Muttaqha Rabe Darma 

Daga Imrana Abdullahi
Ministan ma’aikatar gidaje da raya birane Injiniya Dokta  Muttaqha Rabe Darma, ya bayyana shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda yake kokarin samar da ingantaccen sahihin gyara a jihar Katsina da kasa baki daya.
Kamar yadda ministan Dan asalin Jihar Katsina ya ce shi baya karya kuma baya cika baki amma kuma zai gaya wa mutane ainihin gaskiya a kan dukkan lamarin da zai fadi.
Dokta Muttaqha Rabe Darma ya ce a iyakar gaskiyarsa da saninsa, Allah ya kawo Bola Tinubu ne a lokacin da zai ceci Najeriya daga halin da take ciki.
“Gyara Malam Bola Ahmed Tinubu yazo yi wa Najeriya don haka ba ruwansa da tunanin wanda ba shi da lafiya ayi masa kaza da kaza shi ne dai dai, saboda haka mutanen jihar Katsina za mu gaya masu inda aka nufa domin kowa ya gane cewa Bola Ahmed Tinubu ya kawo ci gaba a arewa da kasa baki daya.
A game da batun irin yadda gidaje ke tsada kuwa sai ya kada baki ya ce, “gaskiya ne gidaje na tsada domin ko shi a ranar da ya shiga ofis ranar Litinin na fadi a gaban kowa na ce gidaje na tsada domin bai yiwuwa Gwamnati ta gina gida Sannan a sayar da shi Naira miliyan 25 sannan ace a yi ne domin masu karamin karfi, kamar yadda ma’aikata ta gaya Mani an gina gidaje a wasu jihohi kamar misalin Jihar Katsina idan aka gina gidaje sai jihar Katsina ta saye gidajen gaba daya sai ta biya wadancan gidajen sai su yi wa jama’a ma’aikata rangwame su ba su gidajen sai a rika cirewa ma’aikatan kudi a cikin albashinsu a hankali a hankali, saboda haka irin wannan hadin kan da sauran mutane musamman yan kasuwa domin Yan kasuwar Najeriya suna da damar da za su yi irin wannan gine- genen domin daman sun saba yin su.
“Duk da akwai wadansu abubuwa da dama da suke zama masu tarnaki kamar misalin tarnakin filaye da dai sauran wadansu abubuwa da dole sai da su ake gina gidaje don haka sai su zo mu hada kai baki daya mu rage masu duk wani tarnakin ta yadda idan su kadai ne suka gina gidajen za su sayar miliyan Talatin To, idan an hada kai sai a sayar da shi miliyan sha biyar ko sha Bakwai sakamakon irin hadin kan da aka yi tare.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka Yayin Da Zamfara Ke Cika Shekaru 30

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.