Home / Labarai / Na Roki Ayi Hanyar Zariya Zuwa Fambeguwa – Yusuf Bala Ikara

Na Roki Ayi Hanyar Zariya Zuwa Fambeguwa – Yusuf Bala Ikara

 

Dan takarar kujerar Sanata a zaben fidda Gwanin da ya gabata karkashin jam’iyyar APC, Honarabul Yusuf Bala Ikara, ya bayyana cewa shi da kansa ya roki Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Malam Kwamared Uba Sani domin ayi hanyar da ta tashi daga garin Zariya zuwa Fambeguwa domin kowa ya amfana.

Honarabul Yusuf Bala Ikara ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyon da ya saki tun bayan kammala tattaunawarsu da manema Gwamnan Jihar Kaduna a kan ta kaddama da cece- kucen da ke ta yada bayanai ka cewa sun karbi makudan kudi domin sasantawa da Gwamnatin Jihar Kaduna tun bayan da aka hana su tsayawa takara a lokacin zaben fitar da yan takarar karkashin jam’iyyar APC a kwanan baya.

Sai dai Yusuf Bala Ikara ya kara da yin cikakken bayani game da lamarin inda ya ce, Daman abin da aka tattauna a cikin taron da aka kira yan takara a dakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kaduna shi ne za a mayar wa da kowa ne dan takara na Sanata da dan majalisar wakilai kudinsa da ya sayi Fom din tsayawa takara za kuma a ba kowa Miliyan biyar a kai.

” Daman Ni tun a wurin taron da aka fito na ce ban gamsu da irin abin da aka tattauna ba a kai, sai aka kara kiran mu yan takarar Sanata taro a gidan Gwamna a Abuja, mun zauna da wasu da suka yi takarar wasu kuma ba sa nan in da aka kara ba mu hakuri aka kuma yi mana cikakken bayanin halin da jihar Kaduna ke ciki, kuma aka ba mu karin kudi Naira Miliyan biyar, wato aka ba Ni Naira miliyan Talatin kenan na biya kudin Fom miliyan Ashirin sai aka kara Mani miliyan Goma a kai, wannan shi ne abin da ya faru ba kamar yadda ake ta yayatawa ba har ana rubuta wa a kafafen shafukan sada zumunta na yanar Gizo cewa an ba mu makudan kudi an sasanta da mu”, in ji Yusuf Bala Ikara.

Ya ci gaba da bayanin cewa a nan ne, “Na yi rokon cewa ayi mana hanyar da ta ratsa kananan hukumomi Uku a yankin Shiyya ta daya shi ne daga Zariya zuwa Fambeguwa, kuma nan take Gwamnan ya kira ministan ayyuka na Tarayyar Najeriya sakamakon cewa aikin na Gwamnatin tarayya ne, an kuma yi maganar aikin a gaba na”.

” An kuma ba Ni damar in bayar da sunayen mutane Uku da za a ba mukamai a Jihar Kaduna kuma tuni aka ba mutane biyu saura daya duk an yi hakan ne lokacin da muke yarjejeniyar samun sasanci tsakanin yan takara da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC.

Saboda haka Ni Yusuf Bala Bala Ikara nake tabbatarwa da jama’ar mazabar Shiyya ta daya wato yankin Zariya da jama’ar duniya baki daya cewa ba wasu makudan kudin da wani ya ba Ni lokacin yin sasanci da Gwamnati da jam’iyyar APC kuma a matsayin mu na ya’yan jam’iyyar APC za mu ci gaba da kokarin ganin an samu nasara a dukkan zabi kan da za a yi.

” Ya dace jama’a da su sani cewa akwai fa Yan takarar da suka kashe makudan miliyoyin kudi lokacin takarar su amma ba a ba su ko rabin abin da suka kashe ba duk da an sasanta, kamar Ni Na kashe kudi sosai lokacin da na tsaya takara amma ba a ba Ni Ko kashi ashirin na abin da Na kashe ba, ina ban da miliyan Talatin din da aka ba Ni saboda haka ta yaya za a rika yada bayanan da ba haka suke ba, mu dai yan jam’iyyar APC ne kuma muna yi wa Gwamnati da jam’iyyar biyayya.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka Yayin Da Zamfara Ke Cika Shekaru 30

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.