Home / Big News / Siyasa Ba Sana’a Bace – Saminu Turaki

Siyasa Ba Sana’a Bace – Saminu Turaki

 

Daga Imrana Abdullahi

 

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki, ya bayyana cewa siyasa ba Sana’a Bace saboda haka masu ganin za su shiga siyasa domin samun abin duniya hakika wannan kuskure ne babba suke aikatawa.

Saminu Turaki ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan rediyon Sawaba da ke garin Hadejia.

Saminu ya ci gaba da cewa idan mutum na da wata sana’ar da yake yi idan ya na son fitar da Zakka sai ya shiga siyasa, amma ba shiga siyasa domin neman kudi ba.

Tsohon Gwamnan na Jigawa Saminu Turaki ya kuma fayyace cewa canza kudin kasa lalata tattalin arzikin kasa ne da ke haifar wa da duk ƙasar da hakan ta faru matsala.

Sai ya bayar da misalin cewa a can shekarun baya Naira ta Najeriya darajarta ya kai dala uku, amma tun da aka fara canza kudin Najeriya sai lamarin ya zamarwa kasa matsala.

Ya ce, “ai marigayi Sani Abacha ya taba ba jami’an Bankin duniya misalin darajar Naira, inda ya ce a dauko dala dari a babban bankin kasa Najeriya aka sayo kayan marmari aka zube a kan teburi nan take ya tambayi jami’an Bankin duniyar da suka zo Najeriya inda ya tambaye su cewa wannan kayan da aka zube a kan teburi nawa suke a kasar ku suka amsa masa da cewa dala dari uku nan take ya ce masu to a nan kasar mu kunji kudin don haka su shugabanni dole sai sun ja damarar kare darajar kudin kasar su.

Ya kara dacewa sau da yawa a Najeriya sai gyara yazo da barna, ko a lokacin shekarun baya da aka yi canjin kudi mutane da dama sun mutu domin ba su da kudin da za su ci abinci.

Turaki ya kara da cewa duk da, “Bola Tinubu amininsa ne amma ya yi wani kuskure na taba wadansu jiga- jigan bangarorin tattalin arzikin kasa a lokaci guda, wato Taba bangaren Man fetur,hana ba masu hada haɗar kasuwanci babban bankin kasa ya ba su dala sai kuma batun taba bangaren wutar lantarki, a tsarin neman gyaran tattalin arzikin kasa ba a taba su a lokaci guda.

“Allah ya jikan Sani Abacha a lokacinsa yaki amincewa da ayi tsarin bayar da wutar lantarki na Ban A,B,C ko D nan take ya ce ba zai yi ba domin hakan ba zai taimaki jama’a na can kasa ba idan an yi irin wannan tsarin.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.