Home / Big News / Jam’iyyar APC,Tinubu Da Uba Sani Ne Za Su Lashe Zabe A 2027 – Musa Bawa Ciki Da Waje

Jam’iyyar APC,Tinubu Da Uba Sani Ne Za Su Lashe Zabe A 2027 – Musa Bawa Ciki Da Waje

…..Baffa Babba Dan Agundi ya bayar da yakin zamani a Kaduna
Daga Imran a Abdullahi
Sakamakon irin yadda Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani ke tafiyar da jagoranci domin inganta rayuwar al’umma hakan ya sa ba tare da shakka ko wata tantama ba a shekarar 2027 su za su lashe zabe da gagarumin rinjaye.
Shugaban kungiyar APC Ciki da waje na Jihar Kaduna da ke fafutukar ganin Tinubu da Uba Sani sun sake cin zabe Musa Bawan FCNA ya tabbatarwa da duniya cewa ba tare da wata tantama ba jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani za su lashe zaben cikin sauki.
Ga dai irin Takin zamanin da aka raba a Kaduna daga hukumar da Baffa Babba Dan Agundi ke yi wa jagoranci
Sai dai ya ce babban dalilinsa na yin wadannan kalamai shi ne irin yadda Gwamnatin tarayya da Gwamna Uba Sani ke yin aiki dai dai Gwargwadon iko da nufin inganta rayuwar jama’a.
“Babu wasu yan Adawa a halin yanzu da suke iya yin wata hobbasa domin a koda yaushe sai dai ka gansu suna canza jam’iyya daga wannan zuwa waccan kawai abin da ke tabbatar da cewa ba su da tudun dadawa, don haka jam’iyyar APC kawai ita ce mafita”.
Musa Bawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da rabon Yakin zamani da za a ba kungiyoyin da ke yin aiki tare da kungiyar APC Cikin da waje a Jihar Kaduna.
Yakin dai an kawo shi ne daga ofishin Daraktan Janar national productivity Center Abuja, mai kula da Shiyyar arewa maso Yamma, da ta ƙunshi jihohi Bakwai,Dokta Baffa Babba Dan agundi da aka ƙaddamar a Kaduna.
Dokta Baffa Babba Dan Agundi dai ya kawo Takin zamani mai suna Nagari kuma an kaddamar da buhuna dari biyu da za a raba wa wadannan ya’yan kungiyoyi daban daban
Musa Bawa FCNA ya kuma ce wannan rabon kaya ba shi ne karo na farko da ofishin Dokta Baffa Babba Dan Agundi ya kawo aka kuma raba a Karkashin kungiyar APC ciki da waje ba, wannan karo na a ƙalla biyar kenan ana raba wa.
Sai dai a wajen taron an yi bayanin irin yadda za a raba takin inda aka ce a ƙalla akwai mutane 50 daga kowace Marabar dan majalisar dattawa da ke jihar Kaduna a yanki Uku da ake da su da hakan ya kama mutane dari da Hamsin kenan da za a raba wa Takin.
Wasu daga cikin iyayen mu mata kenan da suka halarci taron kaddamar da rabon Takin zamanin da Baffa Babba Dan Agundi ya kaddamar a Kaduna
.
Jama’ar da suka taru a wajen duk sun nuna kin dadinsu da irin kokarin da Dokta Baffa Babba Dan Agundi ke yi na kawo kayan alkairi a jihar Kaduna domin jama’a.
Dokta Baffa Babba Dan Agundi ne da kansa ya halarci wajen kaddamar da rabon Takin zamanin da aka yi a harabar ofishin APC ciki da waje a Kaduna.
Da yake tattaunawa da manema labarai shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna Atiku Sanke wanda ya samu wakilcin sakataren tsare tsare na jam’iyyar APC na Jihar Kaduna Honarabul Kawu Ibrahim Yakasai, godiya ya yi da irin wannan abin arzikin da aka kawo daga Gwamnatin tarayya ta ofishin Dokta Baffa Babba Dan Agundi da aka kawo wa jama’ar jihar Kaduna takin Zamani lallai shugaba da mambobin jam’iyya na godiya kwarai.
Sai Kawu Ibrahim Yakasai ya ci gaba da cewa ko a Jihar Kaduna ma Gwamna Malam Uba Sani ya bayar da umarnin cewa a shiga kowace Gunduma a kowane akwatin zabe a nemo masa akalla mutane arba’in da za a ba yakin zamani kowane mutum daya daga cikin arba’in dinnan da za a samo a akwatin zabe za a ba shi buhuna biyu kyauta domin yin Noma a samarwa kasa da abinci.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.