Daga Imrana Abdullahi
.
Wadansu daga cikin manyan yan Najeriya daga arewacin kasar da kuma wadanda suka yi aiki tare da marigayi Janar Hassan Usman da Kungiyoyi masu kishin Arewa sun shirya babban taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina, Ciroman Katsina, karo na Uku a Kaduna.
A wajen taron shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bayyana Marigayin a matsayin shahararren dan kasa nagari mai kishin al’ummar Najeriya baki daya.
Shugaba Tinubu wanda mai bashi Shawara a kan harkokin siyasa Alhaji Kabiru Umar Masari ya wakilta ya jinjinawa marigayi Hassan Usman Katsina abin da ya bayyana da cewa mutum ne da ya yi wa kasa aiki tukuru iyakar rayuwarsa.
Ministan ma’aikatar Gidaje da bunkasa yankunan karkara Injiniya Muttaqha Rabe Darma ya karanta jawabin shugaban kasa a madadin Kabiru Umar Masari, ya bayyana cewa shi ma da kansa da ya fito daga Katsina ya kasance daya daga cikin iyalan wannan gida na Marigayin don haka suna godiya kwarai da wannan taron.
.”shugaba Tinubu ya yi ayyukan raya ƙasa na gina tinuna da yawa a yankunan arewacin Najeriya da kasa baki daya ya kuma tabbatar an kammala aikin samar da Iskar Gas da za a yi amfani da shi a Kamfanoni da gidaje da aka gina tun daga Ajalinta, Kaduna zuwa Kano a halin yanzu an kammala ginin dari bisa dari, kamar yadda shugaban kasa Tinubu ya bayyana ta bakin minista Muttaqha Rabe Darma a madadin Mashawarcin shugaban kasa Kabiru Umar Masari.
Muttaqha Datma ya kuma bayyana ayyukan shugaba Tinubu a bangaren ilimi da sauran fannonin kasar daban daban duk domin ci gaban rayuwar jama’a a ciki da wajen kasar.
An kuma gabatar da muhimman jawabai a kan rayuwar marigayi Hassan Usman Katsina da masana daga jami’ar Ahmadu Bello Zariya da suka hada da Dokta Usman Bugaje da kuma Farfesa Sadiq suka gabatar
Sai kuma masanin harkokin tsaron Najeriya da ya yi aikin ba shugaban mulkin Soja marigayi Janar Sani Abacha shawara a kan harkokin tsaro wato Mejo mai ritaya Hamza Al-Mustapha da ya yi takaitaccen jawabi a kan irin abubuwan ma’adinan ƙasa musamman na albarkatun ruwa da a nan gaba duniya za ta yi alfahari da su domin muhimmanci su.
Ya Bayyana irin albarkar kasa da ke tattare da madatsar ruwa ta Chadi inda ya tabbatar da cewa akwai wata ƙasa a tafkin da ke zaman Takin da za a iya yin amfani da ita wajen yin Noma domin samar da abinci a kasa.
A wajen taron daya daga cikin iyalan marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wato Babangida Hassan Usman sun yi godiya kwarai da wannan kokarin da aka yi na shirya gagarumin taro domin tunawa da irin abubuwan da mahaifinsa ya yi na ciyar da kasa tare da al’ummar ta gaba.
Zamu ci gaba da kawo maku irin yadda taron ya gudana.
THESHIELD Garkuwa