Daga Wakilin mu A Arewacin Najeriya
Wani fitaccen Dan siyasa daga arewacin Najeriya kuma dan asalin jihar Zamfara jihar da darakta janar na Kamfe din Bola Ahmed Tunubu, Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari ya fito ya shaidawa duniya cewa sai ya kawo babban tarnaki da dimbin matsala ga yakin neman zaben Tunubu a shekarar 2027 mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar da ya yi da manema labarai a cikin wani faifan bidiyo da ya saki domin bayyana matsayar sa da ta dimbin magoya bayansa a game da tafiyar Bola Tunubu a shekarar 2027 mai zuwa.
“Mun sha bakar wahala a zaɓen da ya gabata wajen tallar Bola Ahmed Tunubu a zaben farko da ya gabata, mun yi tallarsa saboda mai gidana da nake girmamawa ministan tsaro Bello Matawalle, amma babbar matsalar ita ce bA a sakamana ba sai kawai aka bar mu haka nan fanko a shanun tashi”.
Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa duk da muna tare da ministan tsaro Bello Matawalle, amma za mu yaki Tunubu ba za mu yi shi ba kuma za mu sanya abin magana lasifika mu bi gari gari mu shaidawa mutane illar Tunubu.
“Mun rigaya mun lissafa illolinsa kuma za mu fallasa su ga jama’a domin kowa ya gujewa sake zaben Tunubu a shekarar 2027 mai zuwa.
” Ko shi Minista Bello Matawalle ya san dalilin da yake tallar Tunubu amma mu ba mu da dalilin yin tallar Tunubu. Ni fa a zaɓen can baya da ya gabata mun yi kokari kwarai domin sai da na rabar da mota a ƙalla guda 45 ga biyar ga jama’a domin kara inganta siyasar Matawalle da shi Tunubu amma ba a saka mana ba sam sai aka bar mu muna ta wahala don haka ana yin siyasa ne domin duniya.
“Muna da kungiya wadanda muka shirya zaratan yakin neman zabe kuma lallai mun kammala shirin fafutukar kawo nakasu ga tafiyar Tunubu, domin fa a can wancan lokacin mun bar iyalan mu tsawon lokaci ba mu gan su ba sakamakon fafutukar yakin neman zabe
“Za mu yi babban taron magoya baya a jihohi a ƙalla mu fara da Jiha shida, mun ta fi da magoya bayan mu, mun tabbatar da cewa mun zagaya ko’ina da ko ina tare da magoya baya su rika tallar kada a zabi Tinubu a rika bin tituna ana gaya wa jama’a illolin Tunubu tun da mun rigaya mun rubuta dukkan abin da za mu gaya wa jama’a”.
“Hakika muna girmama ministan tsaro Bello Matawalle amma lallai muna neman yancin mu tare da hakkin mu baki daya”.
THESHIELD Garkuwa