Home / Labarai / AN GA WATAN SALLAH A NAJERIYA – Sarkin Musulmi

AN GA WATAN SALLAH A NAJERIYA – Sarkin Musulmi

 

….Gobe Juma’a take ranar Sallah
Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Sakkwato na cewa Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Dokta Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin watan Sallah wanda ya kawo karshen watan Azumin Ramadana da al’ummar musulmi suka yi a wannan shekarar.
Mai alfarma Sarkin musulmin ya sanar da hakan ne a wajen taron manema labarai da ya yi a fadarsa da ke Sakkwato.
Inda ya tabbatar da cewa an ga watan a wurare da dama da Yammacin yau Alhamis.
Saboda haka gobe idan Allah ya kaimu za a yi Sallah kenan a duk fadin tarayyar Najeriya.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.