Home / Big News / Ba Mu Da Dan takarar Gwamna A Jihar Kaduna – Shugaban Jam’iyyar NDC

Ba Mu Da Dan takarar Gwamna A Jihar Kaduna – Shugaban Jam’iyyar NDC

….Barista Sani Abbas Ba Shi Ne Dan Takarar Gwamna A NDC ba – Shugaban NDC Na Kaduna
Shugaban jam’iyyar NDC na jihar Kaduna Modecai Sunday Ibrahim, ya fitar da wata sanarwar gaggawa inda ya kira lamarin da cewa ana yi wa jam’iyyar zaton kasa sakamakon irin yadda ake bin shugabannin jam’iyyar NDC a matakin Mazabu ana ce masu su bayar da sunayen mutane Goma – Goma za a saka su a cikin tsarin Kamfe na Barista Sani Abbas wai shi ne dan takarar Gwamna a Jihar Kaduna don haka ba gaskiya ba ne.
Shugaban Jam’iyyar NDC na jihar Kaduna ya bayyana hakan ne a cikin wani dogon jawabi na murya da ya yi wa shugaban jam’iyyar na kananan hukumomi,Mazabu da sauran jama’ar jihar Kaduna.
“Barista Muhammed Sani Abbas Ba dan takarar Gwamnan jam’iyyar NDC na ne, kowa ya sani cewa a ranar 29 ga watan Mayu da ya da ce mu yi zaben fitar da gwanin jam’iyya sai shugaban kwamitin zaben  Farfesa Charles Ofuwala, ya bukace Ni a matsayin shugaban jam’iyyar NDC na Jihar Kaduna da in kira masa yan takarar Gwamna dukkansu ya na son ya yi taro da su domin ko zai samu ya dai-dai ta tsakanin yan takarar kamar yadda kundin dokar zabe na shekarar 2026 ya bayyana, cewa zabe kato bayan kato ko kuma a samu sasantawa wato a dai daita a tsakanin yan takara.
“A wannan ranar ne duk na kira su aka yi ta yin taro aka yi taro aka yi taro har wajen karfe Uku na Yamma ba a cimma burin samun dai dato a tsakanin yan takara ba kuma a wannan ranar ba a yi zabe ba,amma zaben yan majalisun Jiha,tarayya da na yan majalisar dattawa da za su tsayawa jam’iyyar NDC takara duk an yi su.
“Amma sai ga shi ba da jimawa ba a ranar 17 ga wannan watan sai Barista Muhammed Sani Abbas, ya kira Ni cewa ya na bukatar ya ganni sai na je wurinsa na je ne da shugaban jam’iyyar NDC na shiyya ta biyu Honarabul Idris Aliyu muka je da Samuel Bahago da kuma wani ana kiransa Haruna Salisu, muna zuwa gidansa sai yake gaya Mani cewa wai shugaban jam’iyyar ne na shiyyar arewa maso Yamma ne ya ce idan ya same shi ya kira shi wai zai yi magana da Ni.
“Da ya kira shi ko wayar bai shiga ba ne sai Ni na kira shugaban jam’iyya na shiyyar arewa maso Yamma,sai na ce ranka ya dade ka ce idan muna tare da Barista Muhammed Sani Abbas a kira ka, sai ya ce daman ya na son ya yi Mani bayani ne shi ya turo Barista Sani Abbas wurina muyi magana ta fahimta ya gaya Mani damuwarsa da bukatarsa, sai na ce to, nan take sai na kashe waya sai na ce wa Barista Muhammed Sani Abbas na ji abin da shugaban jam’iyya na shiyyar arewa maso Yamma ya ce Alhaji Muhammadu Sani Bakin zowo ya ce Mani sai na ce meye damuwarsa?
“Da ya bude bakinsa sai ya ce Mani wai shugaban jam’iyyar NDC a shiyyar arewa maso Yamma ya ce wai ina ba shi fom na nominashin na Dan takarar Gwamna, wanda aka ba Ni, da ya fadi hakan sai na yi shuru,sai na ce masa ranka ya dade ka san dai ba mu yi zaben fitar da dan takara ba ko a matsayinka na lauya ka san abin da kundin dokokin zabe ya fadi na ce masa na biyu ka san dokar zabe ta ce ayi zaben kato- bayan – kato ko kuma a samu dai daitawa a tsakanin yan takara kuma ba a yi ko daya ba.
“Ta yaya za a yi ka ce wai shugaban jam’iyyar NDC na Shiyyar arewa maso Yamma ya ce in baka fom din tsayawa takara sai na ce masa Ni a fahimta ta shugaban jam’iyyar NDC na shiyyar arewa maso Yamma Alhaji Muhammad sabo bakin Zowo ba zai ta ba ce maka kazo Ni ina baka fom din cewa kai ne dan  takara ba amma sai ya ce wallahi ya fadi hakan da ya ce hakan sai na ce masa to ya kira shi mana da ya sake kira sa, sai ya mika Mani waya da ya mika Mani waya sai na gaya masa cewa ga fa abin da Barista Muhammed Sani Abbas ya ce wai ka ce in bashi fom din cewa shi ne dan takara sai nan take ya ce in SA waya ta yadda kowa zai ji maganar da muke yi , sai ya ce wallahi tallahi ya rantse da zatin Allah shi bai ce ma Muhammad Sani Abbas yazo wuri na in bashi fom din an tsayar da shi takara ba da ya fadi hakan kowa da kowa yaji har shi Muhammad Sani Abbas duk kowa ya ji, sai na kashe waya na ta fi sai ya ce mana don Allah sauran mutanen da muke tare su ta fi waje ya na son zai yi magana da Ni sai na zauna na saurare shi sai ya ce shi tun da ya shigo wannan jam’iyyar daga ADC zuwa NDC ya gane tsakani na da shi babu jituwa amma laifinsa ne amma daga yau ba za a sake yin hakan ba, sai na ce masa Ni ban san cewa akwai wani abu a tsakani na da kai ba, koda ya gama wannan maganar sai muka kama hanya muka ta fi.
“Bayan mun ta fi muna nan me zai faru sai na fara jin cece- kucen – cewa Barista Muhammed Sani Abbas ne dan takarar Gwamnan, nan da nan sai na kira shugabannin jam’iyya gaba daya na yi masu fassarar abin da ke nan ran shugabanni baki daya ya ɓaci sai muka rubuta wasika zuwa Abuja hedikwatar jam’iyyar NDC cewa mu ba mu yarda ayi mana dauki dora na dan takara ba domin ba ayi zabe ba.
“Muna nan muna nan wata rana an gayyace Ni Abuja sai aka sanya Ni a gaba, wai shugaba na kasa baki daya ya ce Ni in bayar da fom aba Muhammad Sani Abbas in ba haka ba za a tsige Ni a matsayin shugaban jam’iyya na jihar Kaduna sai na ce masu wannan matsayin Allah ne ya bani Allah ne kuma kadai zai iya kwace wa daga wurina sannan na ce masu na biyu ta inda aka hau ta nan za a sauka, suka ce me nake nufi, sai na ce masu Fom na Gwamna,da na yan takarar majalisun dokokin Jihar da na tarayya da Sanatoci duk shugaban jam’iyya ne na kasa ya ce a ba Ni don haka Ni ba zan ba su Fom ba amma zan mayarwa da wanda ya ba Ni wato shugaba na kasa, sai suka ce in mayar masa kuma a ranar da na mayarwa da shugaba na kasa da Fom na ce ranka ya dade ga Fom ka ce in dawo da shi ko in bayar a ba wani nan take ya ce Mani shi bai fadi hakan ba don haka ina koma da  Fom, maganar da nake yi ma a yanzu akwai Fom na dan takarar Gwamna a hannu na,muna nan muna nan satin da ya wuce akwai wani yaro, ana kiransa Sanato Danjuma LAAH sai ya yi Mani waya cewa ya na son ya ganni.
“Na ce menene sai ya ce ya na son ya yi zama da shugabannin jam’iyyar NDC na Jihar Kaduna gaba daya domin shi an bashi Fom din na gani ina so wato Fim din nuna bukatar yin takara na dan takarar Gwamna ya cika, kuma na ga takardar da idanu na don haka muna da yan takara kenan sai na ce tun da kana son ganin shugabannin jam’iyya zan tara maka su sai na tara mashi su baki daya ina jin a ranar Juma’a ne muka zauna a sabon Ofis na mu yazo ya gan mu.
“Abin mamaki jama’ar Allah ranar da ya zo sai ya zo da takardar Fom na cewa shi ne dan takara wato,(Nomination Form) a hannunsa ba fom din sha’awar zai yi takara ba fa domin sai ka cika shi sannan ne in an dauke ka a matsayin dan takara shi ne za a baka Fom na cewa kai ne dan takara, amma sai ga shi yazo da Fom na cewa shi ne dan takara a nan take a gaban shugabannin jam’iyya baki daya na tambaye shi cewa shin wane ne ya baka wannan Fom din na cewa kai ne dan takara domin a sani na akwai irinsa a hannu na don haka amsar da ya ba Ni itace wai daga hedikwatar jam’iyyar ne ta kasa aka bashi wannan Fom cewa shi ne dan takarar Gwamna kuma an bashi wanann Fom tun ranar 25 ga watan jiha, wato tun ma kafin ranar da za a yi zaben fitar da dan takara a jam’iyyar mu kenan.
“To, mai sauraro zan so ka yi amfani da hankalinka a kan wannan abin da nake gaya maka da ya gama magana da mu muka yi hoto ya yi sallama ya kama hanyar Abuja ko ya koma Kafanchan ne ban sani ba amma a nawa tunanin tun da ya na zama a Abuja ne ya koma Abuja sai Ni kuma na kama hanya na ta fi Abuja na je ganin shugaba na mayar da wanann Fom don haka abin da ke ciki a yanzu shi ne na yi wa shugaba na kasa da shugaban jam’iyya na kasa da dukkan yan takarar gwamna guda hudu wasika cewa akwai abin da ke faruwa a Jihar Kaduna wanda bai dace ba.
“Akwai tambayoyi guda Goma da na yi masu a turance,ina gani zan saka tambayoyin a kan wannan dandalin na mu domin kowanne ya gani,to don haka kada wani shugaban jam’iyya a kowace karamar hukuma ya amince a yaudara shi domin ba mu da dan takarar Gwamna a Jihar Kaduna don ba mu yi zaben fitar da dan takara ba kowa ya sani kuma ba a yi Sasanci a tsakanin yan takara ba don haka ba wanda zai dora mana wani dan takara har wani ya zo ya yi mana karyar cewa shi ne dan takarar gwamna a NDC, koda wani zai tura wa Barista Muhammed Sani Abbas wannan ya taba cewa in ba shi fom din takarar Gwamna a kan cewa shugaban jam’iyya na shiyyar arewa maso Yamma ne ya ce in ba shi kuma shi da kansa shugaban ya musanta maganar kuma ina da shaidu guda uku don haka duk wani shugaban NDC na kananan hukumomi da ya haɗa masa shugabannin jam’iyya lallai ba wannan maganar domin na ji ya na bi ya na cewa a haɗa masa mutane Goma Goma don haka shugabannin jam’iyyar NDC na kananan hukumomi Gara kuja kunnen shugabannin NDC na Mazabu Kada kowa ya caka kansa wuka a Kore shi baki daya daga jam’iyya.
Dukkan wadannan maganganu sun taso ne sakamakon irin yunkurin da barista Muhammed Sani Abbas ke yi da kuma wani tsohon Sanata daga yankin Kudancin Mista Danjuma LAA, suke yi na zama dan takarar NDC a jihar Kaduna
Lokaci ne kawai zai bayyana mana yadda lamarin zai kasance.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.