Home / Labarai / Gwamna Uba Sani Ya Yi Nasara A Kotun Koli

Gwamna Uba Sani Ya Yi Nasara A Kotun Koli

 

Daga Imrana Abdullahi

Kotun koli a tarayyar Najeriya ta bayyana Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani a Matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar, kotun ta yanke hukuncin ne a yau Juma’a.

Kotun mai Alkalai biyar baki dayansu sula yi watsi da daukaka karar da mai gamayya Mohammed Isa Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP ya yi inda yake kalubalantar ingancin zaben Uba Sani.

Hukuncin da Alkali Tijjani Abubakar ya yi inda ya ce ” mai karar bashi da wani abu muhimmi a game da karar da ya yi”.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.