Home / Labarai / Gwamnan Matawalle ya tabbatar da dokar kisa ga masu bada rahotan siri ga ‘Yan Bindiga

Gwamnan Matawalle ya tabbatar da dokar kisa ga masu bada rahotan siri ga ‘Yan Bindiga

 

Daga Hussaini Ibrahim

 

 

Gwamnan jihar Zamfara Honarabul Bello Matawallen Maradun ya sanya hannu da tabbatar da dokar da ‘Yan majalisar Dokokin jihar suka yi na aiwatar da Kisa ga wanda aka kama da hannu cikin ‘Yan Bindiga Masu Garkuwa da mutane da masu ba ‘yan Bindiga bayanan  sirri a Jihar.

Matawallen Maradun ya sanya ma dokar hannu ne ayau bayan Shugaban Majalisar dokokin jihar Muazu Magarya ya gabatar masa da Dokar a gidan gwamnatin da ke Gusau.

A cikin dokar akwai daurin rai da rai ga masu satar shanu. Kuma za’a kafa akwati na amsar koke daga jama’a a gaban gidan gwamnatin dan zamu nasara kawo karshen ‘Yan Bindiga da masu Garkuwa da mutane.

Gwamna Matawallen ya yi kira ga jama’a da su ji tsoran Allah wajan bada bayani siri a cikin wannan akwatin da Gwamnatin ta ajiye.

Shugaban Majalisar dokokin jihar Zamfara, Honarabul Muazu Magarya ya bayyana cewa, sun yi wadannan dokokin ne da nufin  samarwa al’ummar jihar Zamfara mafita mai dorewa.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.