Home / Big News / Kungiyar Mawallafa Ta Arewa Sun Karrama Babbar Sakatariya Dokas Benjamin Tanko

Kungiyar Mawallafa Ta Arewa Sun Karrama Babbar Sakatariya Dokas Benjamin Tanko

….muna jinjinawa mai girma Gwamnan jihar Kaduna
Daga Imrana Abdullahi
Dokar Inti Benjamin Tanko, babbar Sakatariya ce  mai kula da ma’aikatar wasanni a Jihar Kaduna, ta bayyana gamsuwa tare da yin jinjina ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani bisa irin yadda ya shimfida ayyukan alkairi domin ci gaban al’ummar Jiha da kasa baki daya.
Dokas Inti Benjamin ta bayyana hakan ne jim kadan bayan ta karbi lambar Karramawa daga kungiyar mawallafa jaridu da mujallu ta kasa, “Arewa publishers Forum” da suka karramata a Kaduna.
Ta bayyana jindadin ta da wannan Karramawar da aka yi mata daga kungiyar mawallafa jaridu da mujallu ta kasa ta yi Mani, saboda abu ne da ban yi tsammani ba ko kadan.
“Hakika na gamsu da cewa duk abin da kake yi a duniya musamman a fagen aikin Gwamnati akwai wadansu mutane da suke kallon ka da abin da kake yi, don haka ina godiya da farin ciki kwarai.
Babbar Sakatariya Dokas, ta ci gaba da bayanin cewa ta yi aiki a kamfanin Jarida duk da ba ya dade ba, ta yi tsammanin cewa an mance da ita, “amma sai kuka ba Ni abin al’ajabi har ofishina kun karramani wanda hakan ya kara karfafa Ni kwarai a kan ayyukan da muke yi wanda sai da taimakon mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani muke samun nasarar da muke samu a koda yaushe”.
“Hakika Gwamna Sanata Uba Sani na ba mu cikakken hadin kai da goyon baya a wannan ma’aikatar domin duk abin da muka nema ta fannin wasanni ya na ba mu goyon baya kwarai.
“Kungiyoyin mu na wasanni sun halarci gasar wasanni daban daban akwai wadansu gasannin da dama da Jihar Kaduna ta samu nasara da suka hada da wasan ƙwallon Kwando ta Mata Jihar Kaduna ta samu nasara lashe gasar kuma kungiyar mu ta kwallon Gora sun ta fi kasar Ghana sun yi wasanni da maza da mata duk sun samo nasara duk sun lashe kofunan kuma dun sun dawo lafiya don haka muke cewa mai girma Gwamna mun gode, domin in ba da tallafinsa ba da yan wasanni mu ba za su samu zarafin yin nasarar da suka yi ba a wata ƙasa ma da ba Najeriya ba kuma sun halarci gasar kuma sun yi nasara.
“Don haka ina ce maku na gode saboda wannan Karramawar”, inji Dokas.
.A game da batun cika Gwamnan Jihar Kaduna shekaru Uku a kan karagar mulkin jiha kuwa, sai babbar Sakatariyar ta ce, “ina ta ya mai girma Gwamnan Jihar Kaduna murnar cika wannan shekaru a kan karagar mulki,kuma muna fatan Allah ya yi masa jagoranci a kan al’amuran jihar Kaduna.
Gwamna na kokari a kan harkokin ci gaban al’umma da tsaro ga kuma ayyukan Gina hanyoyi a biranen jiha da karkara duk baki daya ga aikin makarantu da Asibitoci, ko muma a wannan ma’aikatar ba a mance da mu ba, musamman duba da irin yadda ake yin aikin Gyaran filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna ana kara daga darajar filin wasan da a can baya yake daukar mutane dubu sha shida amma a yanzu za a mayar da shi mai daukar mutane dubu Talatin da biyu da hakan zai ba wannan filin wasa damar zamowa cikin filayen wasannin Goma da ke daukar mutane da yawa a Najeriya, hakika wannan abin alfahari ne a wannan ma’aikatar don haka muna yi wa Gwamna fatan alkairi  kuma Allah yasa ya sake lashe zabe karo na biyu.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.