Daga Imrana Abdullahi
An bayyana tafiyar Alhaji Atiku Global Concept Mobilization, 2027 da cewa wani al’amari ne tamkar Jihadi mutane ke yi wa kansu domin samun nasara.
Bayanin hakan ya zo ne lokacin da ya’yan
Kungiyar Unguwar Bada rawa Bakin Boda da ke cikin garin Kaduna suka kai wa shugaban kungiyar Alhaji Atiku Global Concept Mobilization Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ziyarar ban girma da kuma bukatar ayi tafiyar tare da su.
“Hakika matakin da kuka dauka shigar ku wannan tafiya hakika kun yi wa kanku kiyamullaili domin ceton kai ne da zaku yi wa kanku da kanku.
Dokta Suleiman Shinkafi ya ce “ku duba lamarin yadda man fetur ke ta kara kudi koma irin yar yaudarar nan ma ba ayi sai an gama siyasa an yi zabe in za a kara farashin a kara kai tsaye kawai ake ta yin komai”.
ku duba irin yadda lamarin abin da Jihar Neja ke ciki inda matasa sama da arba’in suka rasa rayukansu,wai kawai a kan sun kasance inda wai domin suna yin hakar ma’adinai aka kama su daga baya kuma aka raba su da ransu baki daya.
“Da na ta fi wajen wazirin Adamawa ban ce masa ya ba mu kudi ba domin irin wannan abu da kake yi na gaya masa ceto ne kake yi a kasa baki daya”.
“Lallai ya dace ku hada kai ku ci gaba da yin abin da ya dace a wannan tafiyar da kuka shigar halin yanzu.
“Duk abubuwan da za mu yi lallai tare da ku za mu yi ba za mu bar ku ba, kun shigo cikin wannan juyin juya halin da ake ciki kun yi tunani mai kyau
“Wannan matakin da kuka dauka a matsayin matasa ya nuna cewa kun san lallai a halin yanzu da akwai masu cin amanar Talakawan kasa”.

“Duk wanda ke jin tsoron dauri lallai mutum bai shirya yin juyin juya hali ba a yanayin da kasa Najeriya ke ciki”, inji Shinkafi.
In dai Tunubu ya zarce arewa ta ga ma yawo wallahi
THESHIELD Garkuwa