Home / Labarai / Wata Kotun A Kano Ta Soke Zaben Dan Majalisar Wakilai Na Tarauni

Wata Kotun A Kano Ta Soke Zaben Dan Majalisar Wakilai Na Tarauni

Daga Imrana Abdullahi

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki a Jihar Kano ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarauni, Muktar Yerima (NNPP) sskamakon takardar shaidar makaranta na jabu.

Mai shigar da kara, Hafizu Kawu na jam’iyyar APC ya kalubalanci nasarar zaben Muktar Yerima wanda kotun ta soke ranar Alhamis.

Masu shari’ar a Kotun su uku ta yanke hukuncin cewa takardar shaidar kammala makarantar firamare da wanda ake kara, Muktar Yerima ya bayar ta jabun ce.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.