Home / Labarai / Za A Yi Zaben Kananan Hukumomi A Watan Fabrairu, 2025 A Jihar Katsina

Za A Yi Zaben Kananan Hukumomi A Watan Fabrairu, 2025 A Jihar Katsina

Daga Imrana Abdullahi
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ta sanar da ranar 15, ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin lokacin da za a gudanar da zaben shugabanni da Kansilolin a suk fadin Jihar.
 Shugaban hukumar Lawal Faskari ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Katsina da ya samu halartar wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro a Jihar.
Ya ce an yi wannan sanarwar ne domin tabbatar da abin da doka ta tanadar a harkar zabe.
A lokacin zaben kananan hukumomin ana saran samun zaben shugabannin kananan hukumomi 34 da Kansiloli 361 a daukacin kananan hukumomi 34 na Jihar.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.