Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Hajiya Khadija Muhammadu Bello Gimbiyar Badarawa, ta bayyana nade – naden Sarautar da aka yi a masarautar Badarawa a matsayin wata albarkar da ta saukarwa al’ummar Badarawa, Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.
Gimbiyar Badarawa ta bayyana hakan ne a lokacin da take tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala nade naden Sarautar da aka yi a ofishin Sarkin Badarawa.
Gimbiyar ta ce hakika duk wanda aka naɗa lallai ya yi fice tare da jajircewa wajen taimakon al’ummar kasa kuma ya na da wata alaƙa ta taimakon jama’arsa .
“Wadanda aka naɗa din nan an nemo su ne da kuma wadanda iyayensu suka rasu suna matsayin masu Unguwanni sai aka mayar da madadinsu wadansu ƴaƴansu aka ba wadansu kuma da ba su da manyan yaya sai aka canza masu da wadanda suka cancanta kuma muna yi wa Allah godiya”.
Ta kara da cewa a matsayinta Na wadda ta dade a cikin harkokin al’amuran sarauta a kullum suna cikin azamar yin abin da Yakamata.
“Badarawa sai ta zama babbar masarautar da babu irin ta a jihar Kaduna in Allah ya amince”.
Sai ta ja hankalin wadanda aka naɗa da cewa su yi zama tare da yin aiki tsakani da Allah a farkon farin su baki daya, saboda kamar yadda aka bayyana shi ne an kara wa mutum nauyi ne a kan wanda yake da shi a can baya don haka girma ya karu.
“Kuma cancanta ya sa aka baku wanann sarautar an nemo ku an ga irin yadda kuke taimakon jama’a hakan ya sa aka ba ku don haka duk wanda aka ba lallai hakika an kara masa wani sabon nauyi ne a kansa, a ci gaba daga inda aka fara har sai abin da hali ya yi”, inji Gimbiyar Badarawa.
THESHIELD Garkuwa