Home / Big News / Ma’aikata Na Farin Ciki Da Murnar Nadin Ayuba Magaji Suleiman – Rayyana Isyaku NULGE

Ma’aikata Na Farin Ciki Da Murnar Nadin Ayuba Magaji Suleiman – Rayyana Isyaku NULGE

Daga Imrana Abdullahi
.
Kwamared Bayyana Isyaku Turunku, shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na Jihar Kaduna ( NULGE) kuma odito na kungiyar Kwadagon Jihar Kaduna, ya bayyana cikakkiyar hamdala da godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya nuna wa dimbin jama’a ranar da aka nada shugaban kungiyar Kwadago na Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, Sarautar Marafan Badarawa.
Kwamared Bayyana Isyaku Turunku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala nadin a Kaduna.
Turunku ya ce nadin da aka yi wa Ayuba hakika an yi wa dukkan daukacin ma’aukata ne baki daya saboda ko a bisa tarihi ba a taba samun dama kamar irin wannan ba don haka nadin kwamared Ayuba Suleiman ba abin mamaki ba ne saboda ya cancanta ya samu nadin a fadar Sarkin Badarawa domin duk wanda ya san Ayuba ya san jajirtaccen mutum ne ba Dare ba Rana aikin jama’a kawai yake yi.
“Kungiyar Kwadago fa ta ƙunshi kowane irin ma’aikaci har ma da wadanda ba ma’aikatan ba ma kuma ya na shekaru a ƙalla Takwas ya na shugabanci a hakan kuma ya yi shugabancin kungiyar ma’aikatan Gwaje gwajen al’amuran kula da lafiyar jama’a na tsawon shekaru Takwas din haka mutum ne da ya dade ya na hidimar jama’a don haka mutum ne na jama’a don haka muke yi masa fatan alkairi Allah ya ta ya shi riko.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.