Home / Labarai / Allah Ya Yi wa Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, Walin Shinkafi rasuwa

Allah Ya Yi wa Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi, Walin Shinkafi rasuwa

Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga babban birnin tarayyar Najeriya Abuja na cewa Allah ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi rasuwa.
Marigayin dai kamar yadda wata  sanarwa ta bayyana cewa ya rasu ne a garin Abuja kuma za a yi Jana’izarsa a babban masallacin Abuja da misalin karfe hudu na Yammacin yau Lahadi bayan an yi Sallar La’asar.
Hakika karamar hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara, Arewacin Najeriya da kuma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu sun yi babban rashi domin gurbi ne da aka bari mai wuyar cikawa.
Allah ubangiji ya jikansa da rahama yasa mutuwa hutu ce amin summa amin.

About andiya

Check Also

Nenadi  Usman Ce Shugabar Jam’iyyar Lebo A Najeriya – Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Owerri ta tabbatar da cewa shugabancin Jam’iyyar Labour Party na …

Leave a Reply

Your email address will not be published.