…..Zan Mayar Da Jama’a Su Zama Masu Kudi
Daga Imrana Abdullahi
Sabon ministan gidaje da raya karkara na tarayyar Najeriya Dokta Muttaqha Rabe Darma ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ya taimakawa al’ummar kasa jama’a su fita daga cikin kunci da duk wani nauyi na babu a rayuwarsu.
“Ni duk da ba mai Kudi ba ne amma burina shi ne taimakawa al’umma mutane su fita daga cikin damuwar babu, wanda bai da shi ya zamanto ya na da shi duk da Ni ba mai Kudi ba ne ba, amma Ni kuma so nake in mayar da kowa mai kudi mai kudin dai da zai fita daga cikin talauci”.
Ya kara da cewa wannan matsayin da Allah maɗaukakin sarki ya bashi na sabon matsayin minista a tarayyar Najeriya zai yi kokarin kawo ci gaba a ma”aikatar cikin sauri, domin a cikin watanni biyu zuwa Uku kowa zai ga ne cewa akwai ci gaba a wanann ma’aikatar”.
“Mutane za su ji a jikinsu za kuma su gani cewa lallai an samu ci gaba a wannan ma’aikata, dukkansu za su ji a jikinsu cewa an canza domin yanayi ne na halitta ne.
Ya ci gaba da bayar da misalin cewa, ” da zarar yanayi ya canza mutum zai gane ko dai a ji rana ta yi yawa ko yanayin sanyi sanyi a cikin jikin mutum duk sakamakon canjin da aka samu ne, don haka ina tabbatarwa da jama’a cewa za su ji sauyin da aka samu domin rayuwarsu baki daya za ta inganta, in Allah ya yarda.
THESHIELD Garkuwa