Home / Labarai / Gwamna Uba Sani Ya Raba wa Mutanen Alhuhuda Filayen 92 A Zariya

Gwamna Uba Sani Ya Raba wa Mutanen Alhuhuda Filayen 92 A Zariya

 

Daga Imrana Abdullahi

A wani babban taron da aka yi a dakin taron makarantar Sakandare ta Alhudahuda da ke cikin birnin Zariya Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ta hannun Darakta Janar na ma’aikatar filayen jihar Kaduna KADGIS Dokta Bashir Garba Ibrahim ya mikawa mutane Casa’in da biyu, (92) takardun filayen da gwamnatin jihar ta ba su tun bayan da waccan tsohuwar Gwamnati karkashin Malam Nasiru El-rufa’i ta rushe masu matsugunnin da suka gina a kan filin makarantar Alhudahuda da ke Zariya.

Dan majalisar Jiha mai wakiltar Zariya Honarabul Isma’ila da ake yi wa lakabi da Bola Igge, Jan hankalin wadanda suka amfana da samun takardun filayen ya yi da cewa kada su sayar da takardun da suka samu.
“Kuma a nan gaba zan yi kokarin samun Gwamnan Jihar Kaduna domin a taimaka wa wajen a gina tituna akalla koda guda uku ne a wurin ta yadda zai kara daraja da martaba.
A wurin taron dai an samu halartar wakilan yan siyasa da kuma na Mai martaba Sarkin Zazzau da dai sauran jama’ar karamar hukumar Zariya da dama.
Wurin dai da raba wa jama’ar filayen 92 shi ne Dutsen Abba da ke a karamar hukumar Zariya cikin Jihar Kaduna.
Wannan takardar ita ce samfurin takardun filayen da aka ba su
Mutanen dai da aka raba wa wadannan filayen suna yi murna da farin cikin samun filayen daga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Kwamared Uba Sani.
Wata tsohuwa ma daga cikin su saboda tsananin dadi sai da ta fashe da kukan dadi a gaban jama’a saboda abin da ta ce bayan tsawon shekaru Goma da faruwar wancan lamarin na rushe masu gidaje sai yau Allah yasa Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya taimaka masu da wadannan katafaren filaye

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Halarci Taron Farko Na Liyafar Ƙungiyar ‘Yan Jaridun Fadar Shugaban Ƙasa

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, ya halarci taron cin abincin dare na farko …

Leave a Reply

Your email address will not be published.