Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai shiga cikin tawagar manyan jami’an Nijeriya da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da aikewa birnin Addis Ababa na Habasha, domin gudanar da shirin musayar ƙwarewa da dabarun shugabanci tsakanin Nijeriya da Habasha.
Tawagar Gwamnatin Tarayya za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da haɗin kan Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da wasu gwamnoni.
Ana sa ran tawagar za ta tashi daga Nijeriya ranar Talata, domin halartar taron musayar ƙwarewar shugabanci tsakanin Nijeriya da Habasha, wanda za a gudanar daga ranar 7 zuwa 9 ga Oktoba, 2026.
Sauran gwamnoni da ke cikin tawagar sun haɗa da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq; Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti; Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Bassey Otu; Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke; da Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi.
Ziyarar ta samo asali ne daga ƙudurin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a lokacin ƙaddamar da Shirin Gina Jiki na Ƙananan Hukumomi 774 (N774), wanda aka ƙaddamar a zaman Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa karo na 148, domin hanzarta ɗaukar matakan inganta harkokin abinci mai gina jiki a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.
Gwamnatin Habasha ta samu yabo saboda aiwatar da abin da aka sani da Sanarwar Seqota (Seqota Declaration), wadda ake kallonta a matsayin abin koyi wajen mayar da ƙudurin siyasa na ƙasa kan inganta abinci mai gina jiki zuwa tsari mai haɗin kai, samun kuɗaɗen gudanarwa da kuma ɗaukar alhaki a matakan ƙananan hukumomi.
A shekarar 2015, Gwamnatin Habasha ta ɗauki alkawarin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin girman yara sakamakon rashin ingantaccen abinci, musamman ga yaran da ba su wuce shekara biyu ba, nan da shekarar 2030.
Wannan ƙuduri, wanda aka sanya wa suna Sanarwar Seqota, ana aiwatar da shi ne ta hanyar wani shiri da ya haɗa sassa daban-daban na gwamnati, wanda ma’aikatu tara ke cikinsa.
Waɗannan sun haɗa da Ma’aikatar Lafiya; Ma’aikatar Noma; Ma’aikatar Ilimi; Ma’aikatar Ruwa, Ban-ruwa da Makamashi; Ma’aikatar Mata, Yara da Matasa; Ma’aikatar Sufuri; Ma’aikatar Kuɗi; Ma’aikatar Kwadago da Harkokin Jama’a (MOLSA); da Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido.
Sanarwar Seqota na da taswirar aiwatarwa ta tsawon shekaru 15, wadda aka raba zuwa matakai uku, wato ƙirƙire-ƙirƙire da gwaje-gwaje (Innovation), faɗaɗa shirin (Expansion), da kuma bunƙasa shi zuwa cikakken mataki (Scale-Up).
Ana sa ran musayar kwarewar za ta bai wa Najeriya damar yin nazari kan tsarin Habasha da kuma duba hanyoyin da za a iya amfani da irin waɗannan dabaru wajen ƙarfafa matakan inganta abinci mai gina jiki a faɗin ƙananan hukumomin ƙasar.
SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
6 ga Oktoba, 2026.
THESHIELD Garkuwa