Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da yake na ganin Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta cika alkawarin da ta yi na samar da gidaje masu kyau ga al’ummar kasar injiniya Dokta Muttaqha Rabe Darma ministan ma’aikatar da ke kula da harkokin gina gidaje da raya birane ya kai ziyarar ganin irin yadda ayyukan gina gidajen da gwamnatin tarayya ke yi a Unguwar Lekki da ke cikin jihar Legas a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Indai za a iya tunawa wannan aikin ginin Gidajen na karkashin shirin, “Renewed Hope ne da ke karkashin kulawar babban Bankin lamunin gina gidaje na Gwamnatin tarayya, “federal Mortgage Bank”.
Kuma ziyarar na daga cikin irin rangadin kula da ayyukan gine ginen gidaje, domin tantance yadda ci gaban ayyukan yake ciki domin ƙalla ayyukan a lokacin da ya dace don amfanin jama’ar kasa baki daya.
THESHIELD Garkuwa