…Maganganun Adams Oshiomhole ba su dace ba
.Daga Imrana Abdullahi.
Injiniya Farfesa Kailani Muhammad ya bayyana cewa suna yi wa Allah godiya game da batun murnar ranar Dimokuraɗiyya da ake yi na shekarar bana kasancewar Allah ya raya mu har mun ga wannan lokacin da muke ciki a yanzu.
Farfesa Kailani Muhammad ya kuma yaba wa shugabannin arewacin Najeriya da suka gabata irin su marigayi Sardauna Ahmadu Bello,Makaman da irin su marigayi Azikiwe da ake yi wa kirari da Zik na Afirka Bisa kishin kasa da sauransu da har ake kiran su da sunayen masu kishin kasa domin suna son kasar .
“Irin yadda suka yi zama da jagorantar al’umma duk yadda ake ciki in ma kasar za ta samu matsala ne sai su zauna tare a hada kai domin dai kada kasar ta samu matsala ayi tafiya tare al’umma daya kasa daya, ana tare ana dai tafiya har aka samu ranar 12 ga watan Yuni da ake kira,” june 12″, aka rike son kasa da amana aka ɗauko marigayi Bashir Tofa daga Kano aka yi zabe na gaskiya har marigayi Abiola ya ci zaben amma sai sojoji suka karbi mulkin kasar wanda dalilin ne ma ya sa aka sanya wa wannan ranar june 12, don haka abin da zan ce yau shekaru 27 yau tun daga shekarar 1999 da aka sake dawowa Dimokuraɗiyya, amma sai ga shi yan siyasa na neman su kashe Dimokuraɗiyyar.
“Dalilin da yasa muka yi wannan maganar shi ne dimokuraɗiyyar Gwamnati ce da aka sani ta mutane kuma sai abin da jama’a suka ce, amma a yanzu Dimokuraɗiyyar cikin gida za a yi zabe a cikin gida na jam’iyyu idan wasu sun ci zaben ba za a ba su ba ai an kashe Dimokuraɗiyyar kenan tun daga cikin gidan jam’iyyu na farko kenan,na biyu zabubbuka nan da suka zo babu yanayi mai kyau ba kuma APC ba kawai duk jam’iyyun a haka suke inda wasu tun daga shugabannin Kananan hukumomi har Gwamnoni sun zo sun yaushe mutane ta yaya za a samu Dimokuraɗiyyar?
Ya ci gaba da cewa a gaskiya akwai matsala domin a yanzu ba zabubbuka ake yi ba,idan akwai dimokuraɗiyya talakawa za su iya zuwa wurin Mazabu a akwatunan zabe su yi zabe, duk inda ake kwashe mutane a dauke su ace a kawo kudin fansa wa zai je yin zaɓe a irin wadannan wuraren, ai gaskiyar magana shi ke ba wanda zai je kaga an kashe Dimokuraɗiyyar a nan domin ran kowa gida daya ne.
“Abin da muke cewa shi ne, mu dai muna cikin wanann harka kuma muna yi ne saboda Allah ne don haka muke gayawa shugabanni cewa bai yi latti ba su zo su gyara kowa ya koma ga Allah a rike gaskiya da amana a kuma ta sa Allah a gaba.
Kamar yadda muke fadi tun da dadewa Najeriya kasa ce da ta fi kowace kasa dukiya a duniya bayan ma’adinai ga yawan jama’ar da Allah ya ba mu masu ilimi da kwazo, to, me yasa duk abin more rayuwa Dan Najeriya ba zai samu ba idan za a yi la’akari da abubuwan da Allah ya ba mu da ba talaka a Najeriya a ƙalla dan Najeriya zai iya cin abinci sau uku a rana, yaran sa za su je makaranta a samu kiwon lafiya kyauta ayi hanyoyi ko ta ina talakan da bashi da komi ya samu sauki amma sai wadansu yan tsiraru kawai su kwashe komai su dauki tiriliyan, wancan ya kwashi biliyan Goma kudi dai kawai ake ta kwasa, saboda haka muke yin kira zai a gyara.
“Muma a matsayin mu da muka yi APC muka kawo kungiyar taimakawa Tinubu har muka dawo a matsayin kungiyoyi masu goyon bayan APC na kasa muka yi Kamfe ba wai kudi aka ba mutane ba ga mutane nan duk Najeriya ana ta tambayar mu suna son canza sheka domin tun da muka kammala aikin tallar a zabi Tinubu ba ruwansu da mu ba ko maganar a nada mambobin mu wasu mukamai na Gwamnati ma kai ko wata kwangila ko ta Sisin kwabo ce babu komai har yanzu kaga idan da an ba jama’ar mu wani abu ai mutane za su samu amma ba komai har yanzu.
“Ko kudin da yake ta magana lokacin da ya yi wa kasa jawabi cewa ya na turawa Gwamnoni saboda kananan hukumomi da tsaro, ilimi da sauran ababen more rayuwa ai duk magana ce kawai, idan an duba a halin yanzu ina yancin cin gashin kai na kananan hukumomi da ake magana? Gwamnoni sun rike komai”,Inji Kailani Muhammad.
Ta yaya za ce tsawon shekaru Uku za a rika cewa jama’a ayi hakuri za a ga sauye sauyen da ake yi da aikin ake yi kamar yadda ya dace shekara ɗaya zuwa biyu da komai ya Gyaru a Najeriya don haka a tsaya a kawo doka ta kwarai, idan an ba mutum aiki dole ya yi abin da ake son ayi in kuma bai yi ba a hukunta shi kawai, amma rashin bin doka ya kawo komai baya tafiya dai-dai yanzu abin da muke gani a yanzu ana ta ce mana masu zuba jari za su zo zuba jari, da wannan rashin tsaron ne za su saka kudin su masu zuba jarin su saka kudin su a Najeriya mu fa gaya wa kan mu gaskiya zai yi wuya .
” Ko a kwanan baya sai da ƙasar Amurka ta gargadi mutanen ta da kada su rika zuwa Najeriya kuma a rufe Ofishin jakadancin ta saboda ba tsaro a Najeriya duk duniya kowa ya ji ta yaya wasu za su zuba jarin su a kasar nan. Kuma mu kan mu a Najeriya idan da ana amfani da Injiniyoyi ai da abubuwan da muke da su a kasa kawai da ma’adanai ba sai wasu sun kawo mana wani abu ko zuba jari daga waje ba, muna da kwararrun injiniyoyi ko a Turai ma an san da iya aikinsu mai kyau mai inganci da kuma masu yin aikin Jinya da Unguwar zoma ga masu aikin harkar mulki duk suke aiki a kasashen Turai kai har ma a kasashen Saudi Arabiya da Katar da sauransu duk mutanen mu ne daga Najeriya, amma su Kudu saboda yanayin wuri muna ba shugaba Tinubu shawara har ina mamaki lokacin da naje na same shi kafin ayi zabe a shekarar 2023, na ce masa zaka ci zabe in Allah ya yarda har ma na yi wasa da shi na ke gaya masa mu Nufawa za mu karbe island sai ya ce Mani Dokto Farfesa ka daina rubuta korafi ka bari mu ci zabe to, an ci zabe a haka za a je 2027 aci zabe kowa a yanzu kuka yake yi mutanen mu suna kasa a jihohin Najeriya baki daya har da Abuja suna ta koke- koke.
” A cikin watanni Takwas idan an gyara Abubuwa komai zai Gyaru a daina kashe mutane a samu tsaro Allah ya yi mana wadata ba batun rashi ko talauci a Najeriya ba. Amma batun tallafin nan da ya kawo komai farashi ya yi sama ya dace a rage kudin mai komai ya yi kasa a samu sauki a kasa idan ba mu ji dadin mai ba sai wa? Kasancewar mu na shida da ke samar da Danyen mai a duniya kuma a bangaren iskar Gas mune na Uku a rage kudin kayan masarufi, abinci da komai komai ya yi sauki talakawa su samu sauki.Sannan maganar tsaro ai ba zai yuwu ba sojojin Najeriya suna zuwa batun samar da tsaro a wasu ƙasashe amma Ni abin na ba Ni mamaki ace yau a cikin Najeriya sojojin nan sun kasa akwai mamaki kwarai don haka lallai sai an gyara.
” Mu muna ganin a matsayin Adams Ashimhole na Sanata ya rika maganar NNPC ya na kiran mutane barayi hakika bai dace ba sai ya bari sai an kama mutum da satar tukuna, don haka muna yi masa jan hankali ya daina kiran NNPC gidan barayi kuma idan da Ni ne aka kira zan ba shi amsa a wajen kuma mun ji dadi da majalisa baki daya ta ce abin da ya yi ba da yawunsu ba ne daman halinsa ne kuma ya dace wannan maganar da ake yi na makudan kudi sama da tiriliyan dari biyu sai abada shi a fai fai a gano ina matsalar take ne ina kudin ya bace sai a kawo binciken hukumar NNPC da kuma binciken Majalisar dattawa a ga waye ke karya. Wadannan tsofaffin shugabannin NNPC da suka bar aiki suna da iyali da yaya amma an zo ana ci masu fuska a fili ana kaskantar da su ba dai dai ba ne hakan kasar nan fa duk tamu ce kuma koda mutum Banufe ne, ko Inyamiri ko Bahaushe Allah ne ya kawo muka hadu tare don haka mu gudu tare mu tsira tare
THESHIELD Garkuwa