Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an tabbatar da tarihin harkokin wasannin kwallon kafa ta yadda al’umma masu zuwa a nan gaba za su san me wadansu fitattun yan wasan kwallon kafa su yi domin ciyar da Najeriya tare da kare martabar kasar da jama’arta a idanun duniya ya sa wani shahararren dan jarida da ya yi aiki a kafafen rediyo da kuma Zama edita a babbar jaridar New Nigeria mai suna Andrew Fadadon ya rubuta cikakken tarihin yan wasan kwallon kafa na Najeriya da aka ƙaddamar da kashi na daya a ranar 4 ga watan Yuli, shekarar 2026.
Domin kara karfafawa marubuta litattafai Gwiwa ta yadda za su samu damar dogaro da kansu ya sa Kwamared Ambasada Shettima Yerima, da kansa tare da babbar tawagarsa karkashin shugaban tafiyar “Capacity Movement”, Alhaji Sado, suka halarci babban taron kaddamar da littafin mai dauke da tarihin yan wasan kwallon ƙafan Najeriya da suka shahara suka kuma taka rawar gani ta fuskar nemowa Najeriya martaba da mutunci a idanun duniya.
Shettima Yerima ya shaidawa manema labarai a wurin taron cewa duk wani aikin da ya shafi al’umma lallai a koda yaushe ba zai yi kasa a Gwiwa ba wajen aiwatar da shi a koda yaushe don haka ne ma yaga dacewar taimakawa kokarin marubucin ya yi ta yadda zai kara samu kwarin Gwiwar rubuta wadansu litattafan nan gaba.
Shettima Yerima ya ci gaba da cewa irin wannan aikin rubuta littafin abin a ya ba ne domin akwai dimbin ilimi a ciki kuma yan baya za su samu abin da ya faru a baya domin amfanin su ta fuskoki daban daban don haka lallai abin a tallafa ne kwarai.
Yerima ya kuma yi kira ga daukacin yan jarida da su yi koyi da irin abin da wannan mutum daya daga cikin yan jarida Andrew Fadadon ya yi na rubuta littafi.
Sai dai Ambasada Shettima Yerima ya ce shi a matsayinsa ya na ganin lallai Allah ya halicce shi ne domin kawai ya taimakawa rayuwar bil’adama kuma abin da yake aikatawa kenan na tare da gajiyawa ba.
A wajen taron wadansu mutane da suka hada da Sanata yankin Kudancin Kaduna , shugaban hukumar tara kudin shiga na Jihar Kaduna Jerry Adams da sauran jama’a da dama da suka hada da masu horas da wasanni da shugaban kungiyar al’ummar Igbo mazauna karamar hukumar Cikin duk sun bayar da na su tallafin ta hanyar kaddamar da littafin
THESHIELD Garkuwa