Home / Big News / Za A Fara Aikin Titin Kaduna Zuwa Birnin Gwari – Inji Gwamna Uba Sani

Za A Fara Aikin Titin Kaduna Zuwa Birnin Gwari – Inji Gwamna Uba Sani

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Kwamared Uba Sani ke yi na ganin tattalin arzikin kasa ya bunkasa da kuma samar da ingantaccen tsarin lafiya da dukiyar jama’a Gwamnan da kansa ya sanar da cewa za a fara aikin gina titun da ya tashi daga garin Kaduna zuwa Birnin Gwari da nufin inganta rayuwar al’umma.
Gwamnan da ya sanar da labarin a kan shafinsa  na twitter (*) inda ya ce idan an kammala wannan aikin zai kara inganta harkokin dangantaka tsakanin yankin Arewacin Najeriya da sauran yankuna baki daya na duniya, sannan zai kara bunkasa harkokin Noma, Kasuwanci sannan yankin na birnin Gwari zai kara samun Tagomashi a duniya baki daya.
Gwamnan ya kuma bayyana cikakkiyar gamsuwa da jin dadi tare da yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu Jinjina musamman bisa irin yadda ya amince da wannan aikin ya kuma samar da kayan aikin. Ya kara da bayyana cewa Jihar Kaduna a koda yaushe a shirye take wajen ganin an yi aiki tare da gwamnatin tarayya domin samun nasarar da ake bukata a koda yaushe domin al’ummar mu da kasa baki daya su amfana.
.

About andiya

Check Also

INDEPENDENCE: UBA SANI FREES 27 INMATES, CLEMENCY BENEFICIARIES EXCEED 500

  Governor Uba Sani of Kaduna State has granted clemency to 27 inmates in correctional …

Leave a Reply

Your email address will not be published.